Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Gwamnonin Arewa Maso Tsakiyar Najeriya Sun Kudiri Aniyar Hada Karfi Da Karfe Don Dakile Kashe-Kashen Da Ke Afkuwa A Yankin

Daga hagu zuwa dama: Mohammed Umar Bago (Gwamnan jihar Neja), Abdullahi Sule (Gwamnan jihar Nasarawa), Caleb Muftwang (Gwamnan jihar Filato), Rabarand Hyacinth Alia (Gwamnan jihar Benuwe)
Daga hagu zuwa dama: Mohammed Umar Bago (Gwamnan jihar Neja), Abdullahi Sule (Gwamnan jihar Nasarawa), Caleb Muftwang (Gwamnan jihar Filato), Rabarand Hyacinth Alia (Gwamnan jihar Benuwe)

Gwamnonin Arewa Maso Tsakiyar Najeriya, karkashin shugabanta, kuma gwamnan jihar Nasarawa, Abdullahi Sule, sun sha alwashin dakile yawan kashe-kashen da ke afkuwa a yankin.

Shugaban gwamnonin na jihohin tsakiyar Najeriya ya jaddada cewa ba rikici ne na manoma da makiyaya ba, amma batagarine ke sintirin kashe al'umma da basu yi musu laifin komai ba.

Yace “yaya zamu magance shi, saboda ba zamu bar lamarin yana faruwa loto-loto ba. Dalilin zuwanmu kenan mu fada maka cewa, kaine zaka dauki mataki na tattaro dukkan masu ruwa da tsaki ba tare da al'akari da inda suke ko su wanene ba''.

Gwmana Abdullahi Sule ya bukaci yin amfani da na'urori na fasaha don ganowa da kamo batagari da hukuntasu.

Gwamnan Jihar Filato, Caleb Muftwang da takwararsa na Jihar Nasarawa, Abdullahi Sule
Gwamnan Jihar Filato, Caleb Muftwang da takwararsa na Jihar Nasarawa, Abdullahi Sule

Gwamnan jahar Binuwai, Rabaran Fada, Hycinth Alia, wanda yace shima jaharsa na fuskantar matsalar tsaro, yace ba zasu zuba ido suna kallon 'yan ta'adda na kisan mutane ba.

Rabaran Alia yace ''hadin kai muke bukata a Arewa ta tsakiya don zaman lafiya''.

Gwamnan Jihar Nasarawa da takwararsa na jihar Neja, Mohammed Umar Bago.
Gwamnan Jihar Nasarawa da takwararsa na jihar Neja, Mohammed Umar Bago.

Shi kuwa gwamnan jihar Neja, Umaru Bago, yace shima jaharsa na fama da matsalar tsaro ya kuma jaddada muhimmancin tattaunawa musamman da 'yan ta'adda.

''Yana da muhimmanci mu duba hanyoyin warware matsaloli ba tare da amfani da karfi ba. Ba rikicin makiyaya da manoma bane, ta'addanci ne, kuma ba'a tattaunawa da 'yan ta'adda" in ji shi.

Daga Hagu: Gwamnan jihar Neja, Mohammed Umar Bago, Gwamnan jihar Nasarawa, Abdullahi Sule, Gwamnan jihar Filato, Caleb Muftwang
Daga Hagu: Gwamnan jihar Neja, Mohammed Umar Bago, Gwamnan jihar Nasarawa, Abdullahi Sule, Gwamnan jihar Filato, Caleb Muftwang

A martaninsa, gwamnan jihar Filato, Caleb Mutfwang yace shiyyar Arewa ta tsakiya tana da dimbin arziki don haka dole ne su nemi hanyoyin kare al'umma don samun ci gaba.

“Ya kamata mu farfado da mitin na gwamnonin Arewa ta tsakiya don hadin kai da tunani kan magance matsalolin da suka addabe mu,'' a cewar gwamnan na jihar Filato

Kungiyar gwamnonin jihohin tsakiyar Najeriyan sun kuma bada tallafin naira miliyan dari, don sake tsugunar da wadanda rikicin ya shafe su a kananan hukumomin Bokkos da Mangu.

Gwamnonin jihohin Arewa Maso Tsakiyar Najeriya da sauran mahalarta taron.
Gwamnonin jihohin Arewa Maso Tsakiyar Najeriya da sauran mahalarta taron.

A halin da ake ciki kuma, hukumar lafiya ta duniya ta tallafawa jahar Filato da kayakkyakin asibiti don kulawa da wadanda suka sami raunuka suke kwance a asibitoci ake musu jinya.

Kyayyakin sun hada da bandeji, plasta, bakin allura, auduga, safan hannu da sauransu, sun kai na miliyoyin daloli.

Ga rahoton Zainab Babaji daga Jos din Najeriya.

Gwamnonin Arewa Maso Tsakiyar Najeriya Sun Kudiri Aniyar Hada Karfi Da Karfe Don Dakile Kashe-Kashen Da Ke Afkuwa A Yankin
please wait

No media source currently available

0:00 0:03:27 0:00

Dandalin Mu Tattauna

XS
SM
MD
LG