Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

YOBE: Kotu Ta Yanke Wa Wani Tsohon Soja Hukuncin Kisa Ta Rataya Bisa Laifin Kashe Malamin Addinin Musulunci


Kotu
Kotu

Wata babbar kotun jihar Yobe da ke garin Pataskum ta yanke hukuncin kisa ta hanyar rataya akan jami'in sojan nan Lance Corporal  John Gabriel  da ya hallaka fitaccen malamin addinin musuluncin jihar, Sheikh Bagoni Aisami.

Kotun ta kuma yanke hukuncin daurin shekaru goma a gidan gyaran hali ga abokin aikin sojan mai suna Lance corporal Adamu Gideon da ya taimaka wajen aikata kisan.

Da yake zartas da hukuncin a yammacin yau Talata, Alkalin kotun, mai shari'a Usman Zanna Mohammed, ya ce kotu ta sami John Gabriel da laifin kisan kai, shi kuma Adamu Gideon da laifin taimakawa da ma hadin baki wajen aikata laifin.

Alkalin kotun ya ce mutanen biyu sun kasa tabbatarwa kotun cewa ba sa da laifi, don haka aka yanke masu hukunci daidai da laifinsu.

In za a iya tunawa a watan Agustan bara neaka kama jami'in soja bisa zargin yiwa sheikh Goni Aisami kisan gilla a wani wuri da ke yankin karamar hukumar Karasuwa a jihar Yobe, kusa da garin Gashua bayan da malamin ya ragewa sojan hanya a motarsa daga garin Nguru.

A baya dai anyi ta jan kafa wajen gudanar da shari'ar da ta kai har sai da iyalai da daliban malamin da ma kungiyoyin fararen hula suka yi ta kokawa.

Dandalin Mu Tattauna

XS
SM
MD
LG