A cikin wata sanarwa da ya fitar a shafinsa na X(twitter), Olukoyede ya ce abin damuwa ne yadda dalibai a Najeriya kusan kimanin kaso 7 cikin 10 a Najeriya ke tafka laifuka na yanar gizo.
Shugaban na EFCC ya bayyana haka ne a lokacin da yake karbar tawagar Daar Communication PLC da suka kai ziyarar ban girma a hedikwatar hukumar da ke Jabi, Abuja.
“Muna bukatar hadin kan kamfanin sadarwa irin Daar wajen fadakar da matasanmu kan illolin da ke tattare da aikata laifuka ta yanar gizo, abin damuwa ne a ce kashi 7 cikin 10 na illahirin daliban Najeriya a yau suna aikata laifukan yanar gizo," in ji Olukoyede.
Shugaban na EFCC ya yi kira ga kafafen yada labarai da su tsara shirye-shirye da nufin fadakar da matasan Najeriya game da illolin muggan laifuka musamman wadanda suka shafi yanar gizo.
Shugaban na EFCC ya ci gaba da cewa “wadannan su ne matasan da mu ke sa ran za su zama shugabannin gobe, ya kamata kafafen yada labarai su jajirce wajen wayar musu da kai kan munanan ayyuka da illolin ta’addanci.”
~ Yusuf Aminu Yusuf
Dandalin Mu Tattauna