Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Gwamnonin Arewa Sun Ba Da Naira Miliyan 180 Ga Wadanda Bam Ya Ritsa Da Su A Tudun Biri


Kungiyar gwamnonin Arewacin Najeriya.
Kungiyar gwamnonin Arewacin Najeriya.

Kungiyar Gwamnonin Jihohin Arewa ta bayar da gudunmuwar kudi Naira miliyan 180 ga wadanda harin bam din ya rutsa da su a Tudun Biri, karamar hukumar Igabi ta jihar Kaduna.

A wani yunkuri na kokawa game da ibtila’in da ya faru a jihar Kaduna na sake bam da rundunar soji ta bayyana a matsayin kuskure, wanda ya hallaka rayuka da dama.

Kungiyar ta jajanta wa gwamnati da al’ummar jihar Kaduna kan abin da ta bayyana a matsayin wani lamari mara dadi da ya yi sanadin salwantar rayukan mutane da dama tare da asarar dukiyoyi.

Taron na gwamnonin ya gudana ne a ranar Juma’a a gidan gwamnati na Sir Kashim Ibrahim da ke Kaduna, kuma kungiyar ta gwamnonin na arewa wanda Gwamna Alhaji Muhammadu Inuwa Yahaya na jihar Gombe ya jagoranta, ta mika sakon ta’aziyyarta ga gwamnati da al’ummar jihar Kaduna bisa wannan mummunan lamari da ya jawo asarar rayuka da kuma asarar dukiyoyi, wanda suke bayyana faruwar lamarin a matsayin abin takaici kuma gwamnonin sun kuduri aniyar yin aiki tare domin shawo kan lamarin da magance kara afkuwar haka.

A yayin da ake tattaunawa kan batutuwan da suka shafi rashin tsaro, noma, da hako mai a yankin, gwamnonin sun jaddada aniyarsu na yakar kalubalen da ke addabar yankin na Arewa, bugu da kari, kungiyar ta nuna jin dadinta da yadda gwamnatin tarayya ta sabunta himma wajen magance matsalolin tsaro da suka hada da garkuwa da mutane, fashi da makami, rikicin kabilanci, da ta’addanci.

Gwamnonin sun yi alkawarin tsayawa tsayin daka wajen tunkarar wadannan kalubale ta hanyar inganta hadin gwiwa da hukumomin tsaro, karfafa ayyukan tabbatar da doka da oda, hada kan al’umma, amfani da cigaban fasahar zamani, da gyare-gyaren harkokin mulki.

Sun jaddada muhimmancin magance matsalolin rashin tsaro, kamar talauci, rashin aikin yi, da rashin daidaito tsakanin al’umma, domin tabbatar da dorewar ci gaba a yankin.

Gwamna Muhammad Yahaya, yayin da yake yin Allah wadai da aukuwar harin bam din, ya jadadda daukar matakin gaggawa da gwamnonin yankin ke yi na yaki da rashin tsaro. Ya ba da tabbacin cewa kungiyar a karkashin jagorancinsa ta himmatu wajen gudanar da cikakken bincike kan lamarin Tudun Biri, tare da amincewa da cewa magance matsalar rashin tsaro shi ne mafi muhimmanci ga ci gaban al’ummar yankin baki daya.

Haka zalika, gwamnonin sun kuduri aniyar neman hakki da adalci tare da kuma biyan diyya ga wadanda abin ya shafa kuma sun yi kira da a gudanar da bincike don hana faruwar irin wadannan abubuwa marasa dadi a kasar.

Tuni dai Shugaba Bola Tinubu da Gwamna Uba Sani suka ba da umarnin gudanar da bincike kan lamarin domin gano musabbabin faruwar lamarin da kuma rigakafin faruwar hakan a nan gaba.

Wannan dai shi ne taro na farko da gwamnonin suka yi tun bayan zabensu a babban zabe na watan Mayun 2023.

Wadanda suka halarci taron sun hada da gwamnoni da mataimakan gwamnonin jihohin na Arewa.

Gwamna Uba Sani na Jihar Kaduna, wanda ya karbi bakuncin taron, ya jaddada bukatar hadin kan gwamnonin Arewa domin tunkarar tarin kalubalen da ke haddabar yankin da samar da hanyoyin cigaba don alfanun jama’ar yankin.

Yusuf Aminu Yusif ne ya hada mana wannan rahotan daga Abuja.

Dandalin Mu Tattauna

XS
SM
MD
LG