A karshen wannan mako, shugabanni 14 na kungiyar raya kasashen Gabashin Afrika da ta raya kasashen Kudancin Afrika sun gana a Dar es Salaam domin warware wannan rikici da yaki-ci-yaki-cinyewa sama da shekaru 20.
Shugaban kasar Kenya Willaim Ruto, kuma shugaban kungiyar kasashen Afrika ta Gabas dake halartan taron kolin, ya yi kira ga samar da maslaha ta dindindin.
Ya ce “Haduwar mu a nan na tabbatar da duk mun amince cewa lokacin daukar mataki shine yanzu. Rayuwar miliyoyin mutane sun ta’allaka ne a kan kokarin mu na tinkarar wannan gagarumin kalubale da hikima, da fahimta da tausayawa miliyoyin mutanen da rayuwarsu da makomarsu ya fada cikin rashin tabbas.”
A cewar Majalisar Dinkin Duniya, adadin mutanen da aka kashe a cikin hare-haren ‘yan tawayen M23 tun lokacin da ta kwace garin Goma ya kai mutane 3000. Shugabar Tanzania, Samia Suluhu Hassan, ta yi kira ga tattaunawar da zata hada dukkan bangarori kana ta ce tashin hankalin na yanzu yana shafan harkokin cinikayya da zaman lafiyar yankin.
Ta ce "A matsayin mu na shtagabanni, zamu bar tarihi mara dadi idan muka cigaba da zuba ido lamarin na rancabewa , haka zalika idan an bi tsarin amfani da maslahan Afrika don shawo kan matsalolin Afrika, kasashen mu nada alhaki na bai daya mu tabbatar da magance wadannan matsaloli wanda ke yin mummunan tasiri a kan fararen hula da basu san hawa basu san sauka ba.”
Majalisar Dinkin Duniya ta ce sama da mata ‘yan fursin 100 aka musu fiyade kana aka kona su da ransu yayin karya wani gidan yari a Goma, wanda M23 ke rike da ikon shi a yanzu. Taron kolin hadin gwiwan kungiyoyin kasashen yankuna biyun ya nemi a fara tattaunawa kai tsaye da dukkan hukumomin kasa da wadanda ba na kasa ba, ciki har da ‘yan tawayen M23, wanda gwamnatin DR Congo taki yarda ta shiga tattaunawa da ita a bara.
Dr. Nkere Ntanda shehun malami ne a tsagayar nazarin siyasa a jami’ar Kinshasa.
Ya ce “Abin da ke nan yanzu shi ne, DRC zata hau kan teburi tattaunawa da rauni sosai, inda kungiyar M23 mai samun goyon bayan Rwanda ta mamaye wasu yankunanta. Kuma ina jin cewa za su iya yin magana da wadannan bangarori biyu kuma idan sun yi haka zai kai ga batun raba madafun iko.”
Rikicin na yanzu a gabashin Jamhuriyar Dimokaradiyar Congo ya saka kasashe makwabta a ciki kamar Burundi har izuwa kasar Afrika ta Kudu. Yanzu da ake kira ga kasashen waje su shiga tsakanin, fatar samun zaman lafiya ta ta’allaka ne a kan kungiyoyin kasashen yankunan biyu da kuma yarjejeniyar zaman lafiya ta Luanda-Kenya da ta gaza tabuka wani abin kirki kusan shekaru 2.
A saurari cikakken rahoton cikin sauti:
Dandalin Mu Tattauna