Fada ya barke a yau Talata a gabashin Jamhuriyar Dimokiradiyar Congo bayan lafawar kwanaki 2, inda kungiyar ‘yan tawayen M23 mai samun goyon bayan kasar Rwanda ta afkawa sansanonin rundunar sojin Congo dake kudancin lardin Kivu da asubahi, kamar yadda wani mazaunin yankin da majiyoyin tsaro suka shaidawa kamfanin dillacin labaran AFP.
Yayin wani taro da ya gudana a Asabar din data gabata shugabannin kasahen gabashi da kudancin nahiyar Afrika sun bukaci a gaggauta tsagaita wuta cikin kwanaki 5 ba tare da gindaya wani sharadi ba, inda suke fargabar cewar rikicin daya lakume dubban rayuka tare da raba da dama da gidajensu ka iya fantsama zuwa makwabtan kasashe.
A ‘yan watannin baya-bayan nan cikin hanzari kungiyar M23 ta kwace yankuna da dama a yankin gabashin Congo mai arzikin ma’adinai tun bayan data dauke makamai a karshen shekarar 2021.
Fafatawar ta yau Talata na faruwa ne a kusa da garin Ihusi mai tazarar kilomita 70 daga babban birnin lardin Bukavu da kuma filin saukar jiragen saman yankin mai nisan kilomita 40, a cewar majiyoyin tsaro.
Majiyoyi a yankin sun bada rahoton “fashewar manyan makamai”.
Karin dakarun sojin Congo na nausawa zuwa garin Kavumu, wurin da tashar jiragen saman take wanda kuma ya kasance mazauni ga sansanin sojin dake yankin, a cewar majiyoyin tsaro.
Dandalin Mu Tattauna