Jakadan na jamhuriyar Benin Gildas Agonkan ya bayyana cewa, “Abubuwa da dama marasa dadi sun faru, wadanda suka haddasa salwantar harkoki da dama, wadanda suka janyo matsaloli da kunci a Nijar, musamman a Gaya, muna rokonku gafara domin mu da ku ‘yan uwa ne. Mu ci gaba da addu’o’i, mu roki Allah kadda irin wadannan abubuwa su sake faruwa.”
Ya ce “Amadadin hukumomi da al’ummar kasar Benin baki daya ina kiranku ku yafe mana.”
Jakadan ya yi wannan kira ne lokacin da yake jawabi a yayin wani bikin yaye daliban makarantar horon likitoci da ke Gaya a iyakar kasashen biyu.
Da yake bayyana ra’ayinsa kan wannan al’amari, dan fafutika ta yanar gizo, Oumarou Kante, ya ce akwai Alamar sulhu da yake tunkarowa tsakanin wadannan kasashe biyu, kuma ko wanne ya nuna yana bukata wannan sulhu. Wannan abu ne mai dadi wanda yake dadadawa al’umma zuciyarsu a tambayi juna gafara.
Su ma hukumomin Nijar a makon da ya gabata sun aike da jakadan kasar zuwa Benin, inda tuni jakada Kadade Chaibou ya gabatar wa hukumomin Benin takardun aikinsa.
Tsamin dangantaka a tsakanin gwamnatin Benin da ta Nijar abu ne da ya sama asali a washegarin juyin mulkin Yulin 2023.
Shugaba Patrice Talon na daga cikin wadanda ake zargi da yin gaba-gaba a takunkumin da ECOWAS ta kakaba wa Nijar, sannan barazanar tsaron da kasar ta ce ana fuskanta daga sojojin Faransa ta sa hukumominta rufe iyaka da Benin, matakin da ya jefa al’umomin kasashen biyu cikin halin kunci.
Ana sa bangaren wani tsohon dan majalissar dokokin kasar Nijar Abdoul Moumouni Ghousmane, ya ce da yake yanzu an fara kusantar juna lokaci ya yi da za a janye shingayen da suka hana talakawa sukuni.
Tashar jirgin ruwan Cotonou da ke Benin ita ce gabar teku mafi kusa da Nijar, dalili ke nan ‘yan kasuwar kasar kan sauke hajojin da suka yi oda daga kasuwannin duniya.
Sai dai rikicin diflomasiyyar da ya barke a tsakanin wadanan makwabta ya sa hukumomin Nijar juya akalar hajojin kasar zuwa tashar jirgin ruwan Lome da ke kasar Togo duk da matsalolin tsaron da ake fama da su ta bangaren Burkina Faso.
Ko da yake wannan dambarwa ba ta hana danyen man Nijar ratsa Benin ba ta hanyar bututun da ya dangana da gabar teku.
Saurari cikakken rahoton Souley Moumouni Barma:
Dandalin Mu Tattauna