Ma'aikatar cikin gidan jamhiriyar Nijer ta bullo da jerin wasu matakai da nufin saka tsari a aiyukan kamfanonin tsaro masu Zaman Kansu.
Daga yanzu 'yan kasar Nijer kadai ne ke da 'yancin samun lasisin bude Irin wadanan kamfanoni bayan cike wasu mahimman sharuda.
A karkashin wannan sabon tsari ma’aikatar cikin gida tace za ta rinka gudanar da binciken irin wadanan kamfanoni a kai a kai yayin da doka ta tanadi hukunce hukunce kan duk wanda aka samu da saba ka’ida.
Tuni taron majalissar ministoci na karshen mako ya amince da wannan kudiri sabili kenan aka dibar wa kamfanoni tsaro masu zaman kansu watanni 6 domin daidaita al’amura.
A Nijar Kamfanonin tsaro masu zaman kansu kan bada gudunmowa a harkar tsaron cikin gida musamman a wuraren taron jama’a ko kasuwanni da bankuna ko gidajen attajirai.
A watan Yunin 2024 gwamnatin mulkin sojan Nijer ta rufe irin wadanan kamfanoni kimanin 3 ba tare da bayyana dalilanta na yin haka ba matakin da ya raba dimbin ‘yan kasar da aiyukansu.
Har izuwa makon jiya kamfanonin tsaro masu zaman kansu na gudanar da aiyukansu ne a karkashin lasisin wucin gadi dalili kenan da ofishin ministan cikin gidan Nijar ya kudiri aniyar saka tsari a wannan fanni mai matukar mahimmanci
Za'a a rika bayar da lasisin shekaru 5 da a kan iya sabuntawa sannan ya zama wajibi a gudanar da bincike domin tantance halayyar wanda ke fatan kafa kamfanin tsaro .
Haka kuma daga yanzu haramun ne su gudanar da ayyuka irin na jami’an tsaron gwamnati kamar yadda ya zama wajibi su darajta dokokin amfani da bingogin fararen hula da sauran kayayyakin aikin tsaro da aka lamunta da su a dokance abin da wasu ‘yan kasa ke ganin ya yi dai dai.
Saurari cikakken shirin Souley Moumouni Barma:
Dandalin Mu Tattauna