Hukumomin Libya sun gano akalla gawarwaki 50 da aka binne a wasu kaburbura a hamada a yankin kudu maso gabashin kasar, a cewar jami’ai a ranar Lahadi, a wani yanayi mai tada hankali wanda ya ke da alaka da yunkurin wasu mutane na ketarawa zuwa kasashen Turai ta kasar dake Arewacin Afirkan da ya sha fama da tashin hankali.
Cikin sanarwar da hukumar tsaron kasar ta fitar, a kabarin farko an samu gawarwaki 19 a ranar Jumma’a, cikin wata gona a yankin kudu maso gabashin birnin Kufra, ta kuma kara da cewa hukumomi sun kwashe gawarwakin domin gudanar da bincike don gano musabbabin mutuwar su.
Hukumomin sun kafe hotunan jami’an ‘yan sanda da ma’aikatan lafiya a Facebook yayin da suke tonon kasa inda suka gano gawarwakin da aka nade su cikin barguna.
Kungiyar al-Abreen mai ayyukan jinkai, wacce take taimakawa bakin haure a yankin gabashi da kudancin Libya, ta ce bisa ga dukkan alamu, sai da aka harbe wasu kafin aka binne su bayan sun mutu.
A wani kabarin kuma, an gano gawarwaki 30 da aka binne shi ma a birnin na Kufra bayan da aka kai samame a wata cibiyar safarar mutane, bisa bayanan shugaban hukumomin tsaro a Kufra, Muhammad al- Fadeil, wadanda suka tsallake rijiya da baya sun ce kimanin mutane 70 ne aka binne a kabarin. Ya kara da cewa, hukumomi suna ci gaba da bincike don gano sauran gawarwakin da aka binne a yankin.
Da yammacin ranar Lahadi, hukumomi sun ce sun kubutar da masu kokarin ketarawa zuwa Turai 76 sannan sun cafke wasu mutane 3, wani dan Libya da wasu ‘yan kasar waje 2 bisa tuhumar su da ake yi da tsarewa da kuma azabtar da bakin hauren.
Masu shari’a sun bada umarnin a ci gaba da tsare wadanda ake zargin har sai zuwa lokacin da za a gudanar da bincike.
Dandalin Mu Tattauna