Wannan mataki na zama wata gagagrumar nasara ta baya bayan nan tun lokacin sake barkewar rikicin shekara da shekaru a yaki da sojojin gwamnati.
‘Yan tawayen M23 sun shiga bangaren Kazingu da Bagira na cikin birnin kana suna dannawa zuwa cikin tsakiyar birnin mai yawan mutane miliyan 1.3, a cewar Jean Samy, mataimakin shugaban kungiyoyin jama’a a Kivu ta Kudu. Ya ce an ji harbe-harben bindiga a wani bangare na birnin.
Hotunan bidiyo da aka kafe a yanar gizo sun nuna ‘yan tawayen na tattaki zuwa Bagira. A cikin wani bidiyon, an ji wata Muryar a cikin tana ihu tana cewa: “ Sun kai wurin. Akwai su da dama a wurin.”
Sa’o’i kafin nan, ‘yan tawayen sun yi ikirarin kwace filin saukar jiragen sama na biyu a yankin biyo bayan nasara ta kwanaki, yayin da Majalisar Dinkin Duniya ta yi kashedi cewa tashin hankalin na wannan lokaci a fada da sojojin gwamnatin, ya yi sanadiyar rashin matsugunai ga mutane dubu 350.
Majiyoyin yankin sun ce 'yan tawayen M23 sun killace yankin filin saukar jiragen sama na kasa na Kavumu. Sun kuma bada bayani cewa sun ga wasu sojoji suna tserewa daga garin yayin da ake tsaka da gwabza fada.
Dandalin Mu Tattauna