Taron wanda zai kwashe kwanaki 5 ana gudanar da shi, lokaci ne na tattauna makomar kasar a siyasance, fannin tattali arziki da kuma dukkan batutuwan da suka shafi rayuwar al’umma.
Kimanin watanni 18 bayan juyin mulkin da soja suka yi da ya kawo karshen mulkin farar hula.
Da yake jawabin bude babban taron kasa, shugaban gwamnatin mulkin sojan Jamhuriyar Nijar Janar Abdourahamane Tiani ya gargadi mambobin kwamitocin da ke da alhakin tafiyar da wannan zama a kan cewa, a dukkan maganganun da zasu furta da duk abubuwan da su aikata a yayin wannan taro su tuna da sadaukarwa da al’ummar Nijar ta yi da kuma abin da take jira daga gare su a sabuwar tafiyar da ake shirin farawa, ta yadda a wannan karon za a dora kasa kan turbar da zata ba da damar samun kyakkyawar makoma.
Tiani ya ce bambancin wannan zama da sauran shi ne a wannan jikon ba taron ce-ce-kuce ba ne ko wata tankiyar siyasa ko kuma na ramuwar gayya.
Sarakunan gargajiya na daga cikin na gaba-gaba a wannan haduwa ta tarihi, wacce kuma ke bukatar nutsuwar daukacin wakilan da suka fito daga sassan kasar.
Sarkin Katsinan Maradi, Sultan Ahmed Ali Zaki, ya ce kowa ya san amana ce ta kasa ta talakawa aka daura masa kuma kowa ya yi abu tsakanin da Allah shi ne suke fata ga mutane, ba wata kiyayya, ba wata gaba, su yi aiki da zai sa mutanensu su ci gaba.
Haka su ma wasu ‘yan Nijar sun nuna kyakkyawan fata dangane da shawarwarin da zasu fito daga wannan taro na tsawon kwanaki 5.
Batun wa’adin gwamnatin rikon kwarya da maganar shirya zabubbukan da zasu ba da damar mayar da ragama a hannun fararen hula na daga cikin jerin muhimman abubuwan da ake saran zaman na Assises Nationales zai karkata kan su, don bullo da shawarwarin da a karshe zasu gabatarwa Janar Abdrouhamane Tiani da mambobin CNSP.
Tsofaffin shugabannin kasar Nijar da suka hada da Mahaman Ousman da Issoufou Mahamadou da Janar Salou Djibo sun halarci bikin bude taron na tsara taswirar makomar Nijar da al’ummarta.
Saurari cikakken rahoton Souley Moumouni Barma.
Dandalin Mu Tattauna