Shugaban Amurka Donald Trump ya ba da umarnin kakaba takunkumin tattalin arziki dana tafiye-tafiye a kan mutanen da ke yiwa kotun hukunta manyan laifuffuka ta duniya (ICC) bincike a kan Amurkawa da kasashe kawayenta irinsu Isra’ila.
Matakin da Trump ya dauka a jiya Alhamis, ya dace da ziyarar da Firai Ministan Isra’ila Benjamin Netanyahu ke yi a birnin Washington, mutumin da kotun duniyar ke nema kan aikata laifuffukan yaki a Gaza.
Kotun duniyar (ICC) ta yi allawadai da takunkuman sannan tace “tana bayan ma’aikatanta tare da shan alwashin cigaba da samar da adalci da kyakkyawan fata ga miliyoyn bayin allan da ake zalumta a fadin duniya, a kowane irin yanyi ta tsinci kanta a ciki.”
Kotun hukunta manyan laifuffukan kotu ce ta dindindin da ka iya gurfanar da daidaikun mutane a kan laifuffukan yaki da laifuffukan cin zarafin bil adama da aikata kisan kiyashi da kuma mamayar wani yakin na kasashe mambobin kotun daga wata kasa ko wasu mutane daga cikin al’ummar kasar.
Dandalin Mu Tattauna