Argentina zata janye da hukumar lafiya ta duniya (WHO), kamar yadda fadar shugaba Javier Milei ta bayyana a yau talata, inda zata sahun Amurka wacce ta ayyana ficewarta daga hukumar ta Majalisar Dinkin Duniya a watan da ya gabata.
Shawarar Milei ta dogara ne a kan “katafaren bambancin da ake da shi akan kula da harkokin kiwon lafiya musammanma a lokacin annobar korona,” kamar yadda mai magana da yawun fadar shugaban Argentina Manuel Adorni ya shaidawa manema labarai, inda ya kara da cewa kasar ba za ta kyale wata hukumar kasa da kasa ta yi mata katsalandan a kan diyaucinta ba.”
Haka kuma matakin zai baiwa Argentina karin damar aiwatar da manufofin da suka dace da ita, yayin da take tabbatar da kara samun kudade,” a cewarsa.
Tun bayan hawansa kan karagar mulki a 2023, Melei ke takaicin yadda ake kashe kudaden gwamnati, bayan da ya sha alwashin tabbatar da ba’a samu gibi a kasafin kudin kasar ba bayan shafe shekaru ana wadaka.
Dandalin Mu Tattauna