Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Rikitowar Jirgin Sama Kan Titin Sao Paulo Ya Hallaka Mutane 2

Matukin jirgin da fasinjansa mutum guda sun mutu a hatsarin, wanda ya faru jim kadan bayan da jirgin kirar King Air F90 ya tashi daga filin saukar jiragen sama na Campo de Marte, da ke kula da zirga-zirgar jiragen sama a cikin kasar.

A yau Juma’a wasu mutane 2 suka mutu sakamakon rikitowar da wani karamin jirgin sama yayi kan wata babbar hanya da ke tsakiyar birnin Sao Paulo, cibiyar kasuwancin kasar Brazil, tare da dukan wata motar safa bayan daya zame, a cewar hukumomi.

Ba’a tantance ko jirgin na kokarin yin saukar gaggawa ne jim kadan bayan tashin sa ba. Jirgin ya yi zamiya ta daruruwan mitotci a kan babban titin sannan ya daki motar safar gabanin yayi bindiga, kamar yadda shugaban hukumar kashe gobara Ronaldo Melo ya shaidawa manema labarai.

Matukin jirgin da fasinjansa mutum guda sun mutu a hatsarin, wanda ya faru jim kadan bayan da jirgin kirar King Air F90 ya tashi daga filin saukar jiragen sama na Campo de Marte, da ke kula da zirga-zirgar jiragen sama a cikin kasar.

Fasinjojin motar safa din sun tsallake rijiya da baya, sannan mutane 6 sun jikkata, a cewar Melo.

Dandalin Mu Tattauna

XS
SM
MD
LG