Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Fursunoni Falasdinawa 15 Da Aka Saki Sun Isa Turkiya


An tsara cewa galibin fursunonin za su tafi gudun hijira da zarar an sakesu, inda a Lahadin da ta gabata a birnin Doha, Fidan yace Turkiya na iya baiwa da dama daga cikinsu mafaka.

Fursunoni Falasdinawa 15 da Isra’ila ta saki karkashin yarjejeniyar tsagaita wuta ta Gaza sun isa Turkiya, kamar yadda ministan harkokin wajen kasar, Hakan Fidan, ya bayyana a yau Talata.

“A ’yan kwanakin da suka gabata, wasu Falasdinawa 15 sun iso Turkiya daga kasar Masar bayan da aka sako su,” kamar yadda ya bayyanawa taron manema labarai na hadin gwiwa da takwaransa na Masar Badr Abdellatty.

Ofishin jakadancin Turkiya da ke Masar ne ya baiwa tsaffin fursunonin izinin shiga kasar, a cewarsa.

A gabar farko ta yarjejeniyar tsagaita wutar Gaza an tsara sakin Yahudawa 33 da Hamas ke garkuwa dasu domin sakin fursunoni 1, 900, galibinsu Falasdinawa, da ake tsare dasu a gidajen yarin Isra’ila.

An tsara cewa galibin fursunonin za su tafi gudun hijira da zarar an sakesu, inda a Lahadin da ta gabata a birnin Doha, Fidan yace Turkiya na iya baiwa da dama daga cikinsu mafaka.

A shekarar 2011, Turkiya ta karbi Falasdinawa 11 da aka saki a wani bangare na musayar fursunoni tsakanin Isra’ila da Hamas da ta ba da damar sakin sojan Isra’ila Gilad Shalit domin sakin fiye da Falasdinawa 1, 000 da ake tsare dasu.

Dandalin Mu Tattauna

XS
SM
MD
LG