Kwamishinan hukumar kula da 'yan gudun hijira ta Majalisar Dinkin Duniya, Filippo Grandi, ya shaidawa kamfanin dillancin labarai na afp yayin wata hira a Brussels cewar ba'a fayyace abinda matakin ke nufi ba, don haka yana da wuya ayi sharhi akan irin wannan batu mai daukar hankali.
“Wannan abu ne mai ban mamaki, amma zamu jera muga abinda hakan ke nufi a zahiri,” a cewar Grandi.
Trump ya shelanta shirin a jiya Talata yayin wata ganawa da manema labarai ta hadin gwiwa da Firai Ministan Isra’ila Benjamin Netanyehu, wanda ake karbar bakuncinsa a fadar White House domin tattaunawa.
Dandalin Mu Tattauna