Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Musayar Fursunoni: Hamas Da Isra’ila Sun Shirya Domin Zagaye Na Gaba


Hamas da Isra’ila na daf da gudanar da musayar fursunoni a karo na 5 a gobe Asabar karkashin yarjejeniyar tsagaita wuta ta 19 ga watan Janairu.

Isra’ila da kungiyar Hamas na daf da cigaba da musayar wadanda ake garkuwa da su da fursunoni a gobe Asabar, sai dai mummunan martanin daya biyo bayan shawarar Shugaba Donald Trump ta Amurka ta karbe iko da Gaza ta jefa shakku game da makomar yarjejeniyar sulhun mai raunin gaske.

A yau Juma’a, wata kungiyar Yahudawa masu fafutuka ta bukaci gwamnatin Isra’ila ta dore a kan yarjejeniyar sulhun gabanin musayar wadanda ake garkuwa dasu da fursunoni a karo na 5, duk kuwa da yamutsa hazon da kalaman Trump suka yi a fadin gabas ta tsakiya dama wajen yankin.

Tun bayan ayyanawar da yayi yayin ziyarar da Firai Ministan Isra’ila Benjamin Netanyahu ya kai birnin Washington, Isra’ila ta umarci rundunar sojinta ta shirya domin aiwatar da shirin sauyawa al’ummar Gaza matsugunai bisa “radin kansu”, yayin da Hamas tayi fatali da shirin na Trump inda tace abu ne da “gaba-dayansa ba zai yiyu ba.”

Hamas da Isra’ila na daf da gudanar da musayar fursunoni a karo na 5 a gobe Asabar karkashin yarjejeniyar tsagaita wuta ta 19 ga watan Janairu.

Isra’ila da Hamas sun kammala musayar har sau 4 karkashin gabar farko ta yarjejeniyar tsagaita wutar.

Dandalin Mu Tattauna

XS
SM
MD
LG