Wani babban jami’in Majalisar Dinkin Duniya a Jamhuriyar Demokradiyyar Congo ya fada a jiya Laraba cewa, kusan mutane 3,000 ne aka kashe a wani fada tsakanin mayakan M23 da dakarun kasar a fafutukar neman iko kan wasu muhimman biranen yankin gabashin kasar.
Mataimakiyar shugaban ayyukan Majalisar Dinkin Duniya a Demokradiyyar Congo, Vivian Van de Perre, ta shaida wa manema labarai a wata tattaunawa ta kafar video daga birnin Goma cewa, ayarin MDD na taimakawa M23 sosai wajen kwashe gawarwaki daga titunan biranen. Ta ce, ya zuwa yanzu an kwashi gawarwaki 2,000, wasu 900 kuma na ajiye a mutuwaren asibitoci.
Ta ce, akwai yuwuwar adadin ya karu, saboda har yanzu akwai gawarwakin da suka kumbura barbaje a wurare da dama, kuma hukumar lafiya ta duniya (WHO) ta damu matuka game da yuwuwar barkewar cuta.
A farkon watan Janairu ne dai kungiyar mayakan ta M23 ta karya wata yarjejeniyar tsagaita wuta, ta kaddamar da gagarumin tashin hankali a yankin gabashi mai arzikin albarkatun karkashin kasa, da taimakon sojojin Rwanda. A ranar 27 ga watan Janairun, M23 ta ce, ta kame birnin Goma da babban birnin kasar Kivu da wani birni mai mutane sama da miliyan guda, dubbai daga cikinsu wadanda aka daidaita daga gidajen su a wasu rikice rikicen.
Dandalin Mu Tattauna