Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Ana Cigaba Da Gudanar Da Musayar Fursinoni Tsakanin Isra'ila Da Hamas


Ofer Kalderon, ba-Faranshen Isra'ila da Hamas ta yi garkuwa da shi tare da iyalansa
Ofer Kalderon, ba-Faranshen Isra'ila da Hamas ta yi garkuwa da shi tare da iyalansa

An mika wani ba-Faranshen Isra’ila Ofer Kelderon mai shekaru 54 da kuma Yarden Bibas mai shekaru 35 ga Red Cross a garin Khan Younis dake kudancin Gaza kafin suka koma Isra’ila.

Hamas ta mika ‘yan Isra’ila uku da take garkuwa da su a jiya Asabar, saki na baya baya a cikin jerin musaya karkashin yarjejeniyar tsagaita wuta, da zummar kawo karshen yaki tsakanin Isra’ila da kungiyar ‘yan bindigan Falasdinawa.

An mika wani ba-Faranshen Isra’ila Ofer Kelderon mai shekaru 54 da kuma Yarden Bibas mai shekaru 35 ga Red Cross a garin Khan Younis dake kudancin Gaza kafin suka koma Isra’ila. Bayan sa’o’I an sake ba-Amurken Isra’ila Keith Siegal mai shekaru 65 a tashar jirgin ruwa ta Gaza.

An sace Bibas ne daga Kibbutz Nir Oz a ranar 7 ga watan Oktoba shekarar 2023, lokacin da hamas ta kai harin ta’addanci a Isra’ila tare da matarsa, Shiri da ‘ya’yansu maza biyu Ariel mai shekaru 5 da Kfir mai shekaru 2. Sai dai makomar iyalin nashi na cikin rashin tabbas.

A jiya Asabar Isra’ila ta amince da sako fursinoni 90, a musaya ta hudu. Amma wata kungiyar rajin kare Falasdinawa ta ce adadin mutanen da ake sa ran za a sake a cikin wunin ya kai 183.

Isra’ila ta kuma sake bude iyakar Rafah dake tsakanin Misra da Gaza, wanda zai ba falasdinawa 50 a kowace rana tare da ‘yan rakiya 3 su bar Gaza zuwa karbar magani.

Dandalin Mu Tattauna

XS
SM
MD
LG