Hafsan Hafsoshin Sojin Najeriya Janar Christopher Musa ya bayyana cewa, al’ummar kasar na da gagarumar gudummuwar da za su iya badawa a yunkurin shawo kan matsalar tsaro da ake fuskanta a kasar.
Gwamnatin jihar Kano ta janye zargin da ta yi wa Nuhu Ribadu, mai ba shugaban kasa shawara kan harkokin tsaro na cewa da hannunsa a rikicin masarautar jihar Kano.
Cibiyar inganta aikin majalisar da rajin yaki da cin hanci da rasahwa ta CISLAC, ta bayyana matukar damuwa ga dambarwar dake faruwa na sake maida Sarkin Kano Muhammadu Sanusi na biyu a kan karagar mulki, da kuma sauke Alhaji Aminu Ado Bayero.
Ofishin mai baiwa shugaban kasa shawara na musamman kan harkokin tsaro NSA, Malam Nuhu Ribadu ya musunta zargin tura jami’ai zuwa masarautar Kano.
Yanayi ya fara dumama a birnin Kano da kewaye sakamakon saukar mai martaba sarkin Kano da gwamnati ta cire Alhaji Aminu Ado Bayero a filin sauka da tashin jiragen sama na Kano.
Masu tada kayar bayan sun yi watsi da ayyukan ta'addanci tare da mika wuya ga sojojin ne a jiya Alhamis 23 ga watan Mayun da muke ciki.
Mai Shari'a Yellim Bagoro ne ya bada umarnin a jiya Alhamis 23 ga watan Mayun da muke ciki, sakamakon bukatar da lauyan Hukumar EFCC mai yaki da masu yiwa tattalin arzikin Najeriya zagon kasa, Bilkisu Buhari, ta gabatar.
An mayar da Sanusi Muhammadu a matsayin Sarkin Kano bayan ya karbi takardar nadinsa daga Gwamna Abba Yusuf ranar Juma'a.
Mai shari’a Mohammed Liman ne ya mika wannan umarnin ga gwamnatin ta Kano.
Domin Kari
No media source currently available
A jawabin da ya gabatar, shugaban kasar, Bola Tinubu ya ce gwamnatinsa na samun nasarar yaki da ta’addanci da kuma ‘yan fashin daji. Jawabin shugaban ya zo ne adaidai lokacin da matasa a wasu sassan Najeriya suka gudanar da zanga-zangar matsin rayuwa.
Mataimakan ‘yan takarar shugaban kasa, Tim Walz na jam’iyyar Democrat da kuma JD Vance na Republican sun fafata a muhawarar su ta farko wacce kuma ita ce kadai da za su yi kafin zaben shugaban kasa a watan Nuwamba. Ga fasaarar rahoton Tina Trinh daga New York.
A bana, sau biyu ana yin yunkurin halaka dan takarar shugaban kasa na jam’iyyar Republican Donal Trump. Muryar Amurka ta ji ta bakin wasu Amurka da suka mallaki bindiga wadanda suka ce yunkurin halaka Trump din bai sauya matsayarsu ba a game day dokokin mallakar bindiga a Amurka.