Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

An Samu Nasarar Kashe 'Yan Bindiga Da Barayin Daji 9,800 Cikin Shekara Guda - Ministan Tsaro


Ministan tsaron Najeriya Badaru Abubakar
Ministan tsaron Najeriya Badaru Abubakar

Ministan Tsaron Najeriya, kuma tsohon gwamnan jihar Jigawa, Badaru Abubakar a hirarsa ta musamman da Shugaban Sashen Hausa na Muryar Amurka, Aliyu Mustapha, ya tabo batuttuwa da dama game da tsaro musamman a arewancin Najeriya.

Badaru ya ce tun ya fara aiki, ya gana da dukkan manyan tsoffin sojoji da ma’aikatan tsaro, ciki harda tsohon Shugaban mulkin sojin Najeriya, Abdulsalam Abubakar, don samun shawarwarin magance matsalar tsaro.

Albarusai da makaman da aka samu a motar wadannan 'yan bindiga bayan da aka kashe tara daga cikinsu, aka kama guda biyu
Albarusai da makaman da aka samu a motar wadannan 'yan bindiga bayan da aka kashe tara daga cikinsu, aka kama guda biyu

Ya kuma nanata cewa babban matsalar tsaro shine rashin haddin kan shuwagabannin tsaro, amma ya zuwa yanzu, an samu haddin kai a tsakanin shuwagabannin na tsaro da suka hadda da ‘yan sanda da jami’an fararen hula wanda shine tushen nasarorin da ake ta samu.

Ministan tsaron Najeriya Badaru Abubakar
Ministan tsaron Najeriya Badaru Abubakar

Ya kara da cewa cikin shekara dayan da aka cika, an samu nasarar kashe ‘yan ta’adda da barayin daji kusan 9,800, an kuma kama kimanin 'yan bindiga 7,000, sannan kuma an kwato mutanen da aka sace kusan 4,700.

Badaru ya ce babban matsalar da su ke fuskanta shine na samun haddin kan jama’a wajen bada ingantaccen bayanai.

Saurari cikakken hirar a sauti:

please wait
Embed

No media source currently available

0:00 0:24:57 0:00

Dandalin Mu Tattauna

XS
SM
MD
LG