A cikin makon nan ne shugaban Majalisar Dattawan Najeriya, Godswill Akpabio, ya sanar da amincewar shugaban kasar Najeriya, Bola Tinubu, kan batun samar da Hukumar Raya Jihohin Arewa Ta Tsakiyar Najeriya ko North Central Development Commission (NCDC) a turance, da zummar inganta tattalin arzikin al'ummar yankin da samar da ababen more rayuwa ga al'ummar yankin da suka sha fama da tashe-tashen hankulan da suka daidaita su.
Jihohin da sabuwar hukumar ta NCDC za ta dubi matsalolinsu su ne Kogi, Neja, Kwara, Binuwai, Nasarawa da Filato.
Sanata Istifanus Gyang da ya wakilci Filato ta Arewa a Majalisar Dattawa daga shekara ta dubu biyu da goma sha tara zuwa dubu biyu da ishirin da uku (2019 - 2023) ya ce sun yi tunanin a kirkiro da hukumar ne, ganin yadda yankin ya sami komo baya.
Mai sharhi kan lamura a jahar Nasarawa, Kasimu Ali, ya ce shiyyar Arewa ta tsakiyar Najeriya mai fadin murabba'in mita dubu dari biyu da talatin da biyar (200,035)da a kalla mutane miliyan ishirin da tara (29,000,000) kuma dukkan jihohin na dankare da ma'adinai daban-daban da ake bukata da duniya, don haka ya shawarci hukumar ta samar da masana'antu.
Duk da yawan jama'a da dimbin arziki da ke yankin, matsalar tsaro ta yi kamari inda a sassa daban-daban aka kashe mutane da dama kuma aka raba wasunsu da matsugunansu.
Madam Josephine Habba, daraktar hukumar samar da zaman lafiya a jahar Binuwai, ta ce ricikin da ke aukuwa a yankin tun shekaru fiye da goma, ya sanya al'umma da dama yin gudun hijira don haka take fatan hukumar ta maida mutane garuruwansu don ci gaba da rayuwa.
Al'ummar shiyyar Arewa ta tsakiyar Najeriyar dai ta bukaci hadin kai tsakanin gwamnatocin tarayya, jihohi da kananan hukumomi da duk masu ruwa da tsaki don warware matsalolin da suka addabi yankin.
Saurari cikakken rahoton Zainab Babaji:
Dandalin Mu Tattauna