An sace Tsiga ne, tare da dimbin mazauna kauyen Tsiga da ke karamar hukumar Kankara ta jihar katsina.
Wani mazaunin yankin ne ya tabbatarwa tashar talabijin ta Channels da afkuwar lamarin ta wayar tarho a yau Alhamis.
Yace, al’amarin ya faru ne a jiya Laraba bayan da batagarin dauke da muggan makamai suka mamaye gidan tsohon babban daraktan hukumar ta NYSC.
Ganau sun bayyana cewar tsohon shugaban hukumar ta NYSC na cikin mutanen da maharan suka yi garkuwa dasu.
Wasu majiyoyi sun shaidawa tashar talabijin ta Channels cewa yayin harin wanda ya faru cikin mintuna, an raunata wasu mazauna kauyen 2 sannan daya daga cikin ‘yan bindigar ya mutu bayan da wani danuwansa ya harbe shi bisa kuskure.
Har yanzu gwamnatin Katsina da rundunar ‘yan sandan jihar ba su fitar da sanarwa game da satar mutanen ta baya-bayan nan ba.
Dandalin Mu Tattauna