Shugaban Najeriya Bola Tinubu ya bar Abuja zuwa birnin Paris, na kasar Faransa.
Mashawarcin shugaban kasar na musamman akan harkokin yada labarai da tsare-tsare, Bayo Onanuga, ne ya bayyana hakan a sanarwar daya fitar a yau Laraba.
A cewar Onanuga, ziyarar shugaban zuwa kasar da ke nahiyar Turai ta kashin kai ce, inda ya kara da cewa Tinubu zai yi ziyarar ne a kan hanyarsa ta zuwa Addis Ababa, babban birnin Habasha.
“Yayin da yake Addis Ababa, Shugaba Tinubu zai bi sahun shugabannin Afrika a taron kwamitin zartarwar kungiyar Au ta kasashen nahiyar Afrika karo na 46 da kuma karo na 38 na taron shugabannin kasashen da zai gudana tsakanin 12 da 16 ga watan Febrairun da muke ciki,” a cewar Onanuga.
“Yayin ziyararsa a Faransa, Shugaba Tinubu zai gana da takwaransa na kasar, Emmanuel Macron.”
Hadimin shugaban kasar ya kara da cewar Tinubu zai isa Addis Ababa a farkon mako mai zuwa domin halartar taron kolin kasashen Afrika.
Dandalin Mu Tattauna