Babban daraktan asusun na NELFUND, Akintunde Sawyer, ne ya bayyana hakan a yayin wata ganawa da manema labarai a Abuja a yau Laraba.
A cewar Akintunde, wannan baya cikin naira biliyan 1 da miliyan 700 da aka biya fiye da dalibai dubu 20.
“A yau naira miliyan 850 za su bar asusun ajiyar NELFUND zuwa manyan makarantu. Wannan ba ya cikin naira biliyan 1 da miliyan 700 da aka riga aka biya.”
Tun da fari, Sawyer ya bayyana cewa asusun NELFUND ya biyawa dalibai dubu 20 kudin karatu zuwa ga makarantunsu.
Ya kara da cewa an amince a biya adadin rancen da ya kai dubu 260 ciki har da kudin makaranta da na kashewar daliban.
Ana sa ran akalla dalibai miliyan 1 da dubu 200 ne zasu ci gajiyar wannan shiri na gwamnatin Shugaba Bola Tinubu.
Dandalin Mu Tattauna