Sanata Titus Zam mai wakiltar mazabaar Benuwe ta arewa maso yamma, gabatar da hujjar cewa za'a iya shawo kan matsalar rikicin manoma da makiyaya ta hanyar yin dokar da zata haramta kiwo a sake a fadin Najeriya.
Gwamnatin Kano na tuhumar Ganduje da mai dakinsa, Hafsat Umar da wadansu mukarrabansa da zargin aikata laifuffuka 10 masu nasaba da cin hanci da almundahana da karkatar da kudaden al’umma na biliyoyin Naira
Da yake gabatar da rahoton yayin zaman majalisar na ranar laraba, Shugaban Kwamitin, Henry Zacharia, yace ba’a yi amfani da galibin basussukan da gwamnatin El-Rufa’i ta ranto akan bukatun da suka sa aka karbosu ba, a yayin da wasu lokotanma, ba abi ka’idojin karbo bashin ba.
Kwamishinan ‘yan sandan jihar Zamfara, Muhammad Dalijan ne ya bayyana haka a lokacin da ya karbi bakuncin jami’in da ke kula da sashin yaki da ta’addanci a karkashin ofishin Majalisar Dinkin Duniya kan yaki da miyagun kwayoyi (UNODC).
Shugaban Najeriya Bola Tinubu ya umurci Ministan Kudi na kasar, Wale Edun, da ya gabatar da tsarin da gwamnati za ta bi na aiwatar da sabon adadin albashin ma’aikata mafi karanci.
Masu ba da lamuni a Najeriya sun fara gabatar da tsare-tsaren cika sabbin sharuddan gudanar da hada-hadar kudi da babban bankin kasar ya bullo da su a watan Maris don karfafa hada-hadar kudi.
Jami’an ‘yan sandan shiyar Tudun Wadan Zariya ne suka kama wanda ake zargin, mai suna Hussaini a unguwar Tudun Jukun sakamakon samun sahihan bayanan sirri game da take-takensa.
Al’amarin daya afku da misalin karfe 9 da rabi na safiya ya hada da wata tanka da ake zargin tana dauke ne da iskar gas wacce ta latse wata karamar mota tare da tarwatsewa a yayin da take kokarin shiga shatale-tale.
Ko da yake har yanzu babu cikakken bayanai kan harin, sai dai hukumomin sojin sun tabbatar da hakan a wata sanarwa da suka fitar a ranar Talata.
Shugaban kungiyar kwadago ta TUC Festus Usifo ne ya tabbatar da hakan a yau Talata a Abuja bayan wata ganawar hadin gwiwa na majalisar kolin manyan kungiyoyin kwadagon Najeriya 2.
Rahotanni daga kauyen farin Doki dake yankin Erana a karamar hukumar Shiroro na jihar Neja na nuna cewa, wani makeken rami da masu hakar zinari ke tona wa ya rufta da mutane akalla 50.
Domin Kari
No media source currently available