Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Kudirin Neman Haramta Kiwo A Sake Ya Tsallake Karatu Na 2


Zauren majalisar dattawan Najeriya (Facebook/Nigerian Senate)
Zauren majalisar dattawan Najeriya (Facebook/Nigerian Senate)

Sanata Titus Zam mai wakiltar mazabaar Benuwe ta arewa maso yamma, gabatar da hujjar cewa za'a iya shawo kan matsalar rikicin manoma da makiyaya ta hanyar yin dokar da zata haramta kiwo a sake a fadin Najeriya.

Kudirin neman haramta kiwo a sake tare da kafa killatattun wuraren kiwo a matsayin maganin yawan tashe-tashen hankula tsakanin manoma da makiyaya a Najeriya, ya tsallake karatu na 2, a yau Laraba, bayan da aka dan tafka zazzafar mahawara.

Haka kuma, Majalisar Dattawan ta gabatar da tayin gudanar da taron kuli akan batun, baya ga zaman sauraran ra'ayin jama'a da samun cikakkiyar mafita.

Tayin na zuwa ne bayan da Sanata Titus Zam mai wakiltar mazabaar Benuwe ta arewa maso yamma, ya gabatar da hujjar cewa za'a iya shawo kan matsalar rikicin manoma da makiyaya ta hanyar yin dokar da zata haramta kiwo a sake a fadin Najeriya.

Ya kuma dora hujjarsa akan bukatar bin tsarin da sauran duniya ke tafiya akansa a harkar kiwon dabbobi ta hanyar yin dokar da zata haramta kiwo a sake tare da yin watsi da tsohuwar al'adar nan da aka daina yayi mai cike da hatsari da yawan wahalhalu.

Duk da adawar da kudirin ya ci karo da shi daga wasu 'yan majalisar ciki harda Mataimakin Shugaban Majalisar, Sanata Barau Jibrin, wanda ya nema ganin an yi watsi da kudirin, galibin 'yan majalisar sun bata goyon baya da aka kada kuri'ar murya.

Daga bisani an mika kudirin zuwa kwamitin majalisar dattawan akan noma, ciniki, zuba jari da harkokin shari'a domin dawowa majalisar da rahoto akai cikin wata guda

Dandalin Mu Tattauna

XS
SM
MD
LG