‘Yan majalisar karkashin jagoranci Ikenga Ugochinyere mai wakiltar mazabar tarayya ta Ideato, sun gabatar da tayin wa’adin mulkin shekaru 6 falan 1 ga shugaban kasa da gwamnoni jihohin najeriya 36.
Akalla mutane 50 ne aka kashe tare da yin garkuwa da wasu da ba a tantance adadinsu ba, da suka hada da mata da kananan yara, lokacin da wasu ‘yan bindiga suka kai hari a kauyen Yargoje da ke arewa maso yammacin Najeriya a karshen mako, kamar yadda mazauna garin suka bayyana a ranar Litinin.
Matsalar rashin tsaro na ci gaba da tunzura jama'a a Najeriya har wasu na ganin da ma an mayar da su makwabciyar kasar in har Najeriya ba ta iya kula da kare rayukan su.
Hakan ya biyo bayan komawa kan teburin tattaunawa ranar Laraba bayan kungiyoyin, a ranar Talata, suka jingine yajin aikin da suka tsunduma ranar Litinin da ya gabata.
Gwamnoni 36 dake cikin kungiyar gwamnonin Najeriya sun ce tayin naira dubu 60 da gwamnatin tarayya ta yi ba abune mai dorewa ba kuma ba zai yiyu ba.
Ministan Hajji da Umrah na Saudiyya Tawfiq Al-Rabiah ya sanar da zuwan maniyyatan kusan miliyan daya da dubu dari biyu daga sassa daban-daban na duniya.
Kwamitin alkalai 3 karkashin jagorancin Thomas Okusu ne ya zartar da hukuncin a yau Juma’a.
Dutsinma da Safana na daga cikin kananan hukumomin dake sahun gaba inda ake samun karuwar ayyukan ‘yan bindiga duk da matakan da gwamnati da hukumomin tsaro ke dauka na shawo kan matsalar masu tada kayar bayan a yankunan.
Babban Darkatan Hukumar NEMA, Zubaida Umar, ce ta bayyana hakan a birnin Gusau yayin wani gangamin wayar da kai akan dabarun rage karfin ambaliyar ta hanyar yin gargadi da daukar matakai da wuri.
A kokarinta na karfafa da kuma bunkasa tara kudaden shiga Gwamnatin jihar katsina ta bullo da sabuwar manhajar biyan kudin haraji a jihar.
Domin Kari
No media source currently available