Hukuncin kotun na yau Alhamis ya rushe ko soke sanya hannu akan dokar da gwamna Abba Kabir Yusuf ya yi a ranar da majalisar ta kammala aikinta akan daftarin dokar
Ranar 20, ga watan Yuni na kowace shekara rana ce da Majalisar Dinkin Duniya ta ware domin duba halin da 'yan gudun hijira suke ciki a sassan duniya.
Adadin wadanda suka kamu da kwalara a fadin jihar ya karu zuwa mutum 401, inda cutar tafi kamari a yankunan Lagos Island da Kosofe da kuma Eti-Osa.
A yau Alhamis, hadimin Shugaba Tinubu Olusegun Dada ya wallafa a shafinsa na X cewar, Shugaban Afrika ta Kudu Cyril Ramaphosa da Bola Tinubu na Najeriya sun gudanar da tattaunawar kasa da kasa akan harkokin diflomasiya da tattalin arziki bayan kammala bikin rantsar da ramaphosan.
Rundunar sojin Najeriay ta ce za ta sayo sababbin jiragen sama 50, domin kara karfin ta na yaki da ‘yan ta’adda a yankin Arewa masu yamma na kasar.
Keyamo, yace an riga an cimma yarjejeniya tsakanin Shugaban Najeriya Bola Tinubu da takwaransa na Hadaddiyar Daular Larabawa Muhammad Bin Zayed Al-Nahyan a ziyarar da tinubun ya kai kasar a watan Satumbar bara.
Tuggar wanda ke jagorantar shirin aiwatar da sabuwar manufar kasashen ketare da Shugaba Tinubu ya kirkiro, yace yarjejeniyar AGAO zai taimaka wa tattalin arzikin kasashen Afirka wanda Amurka ta yi musu rangwame wurin haraji domin basu daman shigo da kayayyaki da aka sarrafa kasuwannin Amurka.
Mahara sun kashe mutane biyar, su ka yi garkuwa da hudu, su ka kuma raunata wadansu mutane biyar a harin ta'addanci da suka kai a jihar Sakkwato ranar Sallah.
Fadar Gwamnatin Najeriya ta ce ba a yi mata adalci ba a rahoton da mujallar New York Times ta wallafa da ya jibinci tattalin arziki da tsadar rayuwa da ake fama da ita a kasar.
Hasashen hauhawar farashin kayayyaki a Najeriya a duk shekara ya kai wata sabuwar kokoluwa na shekaru 28, da ya kai kashi 33.95 cikin 100 a watan Mayu, kamar yadda alkaluman hukuma suka nuna ranar Asabar.
Al'ummar Ghana da tuni suka fusata su ke kokawa kan daukewar wutar lantarki ba tare da shiri ba, sun sake fuskantar karin zullumi bayan da masu rarraba wutar lantarkin suka sanar da karin katsewar wutar lantarki a makonni masu zuwa.
Alhazan duniya kimanin miliyan biyu na gudanar da tsayuwar Arfa a cikin tsananin zafin rana da ya kai ma’auni 46 na selso. Hakan ya sa bukatar alhazan su kaucewa yawan zirga-zirga a ranar don kare lafiyarsu.
Domin Kari
No media source currently available