Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

‘Yan Sanda Sun Kama Wani Dan Shekara 70 Da Ake Zargin Dan Bindiga Ne


Jami’an ‘yan sandan shiyar Tudun Wadan Zariya ne suka kama wanda ake zargin, mai suna Hussaini a unguwar Tudun Jukun sakamakon samun sahihan bayanan sirri game da take-takensa.

Hukumomin ‘yan sanda a jihar Kaduna sun cafke wani mutum mai shekaru 70 da ake zargin dan bindiga ne a garin Zariya. haka kuma sun damke karin wasu mutum 3.

Jami’an ‘yan sandan shiyar Tudun Wadan Zariya ne suka kama wanda ake zargin, mai suna Hussaini a unguwar Tudun Jukun sakamakon samun sahihan bayanan sirri game da take-takensa.

Dan shekara saba'in da ake zargi da ake zargin dan bindiga ne a garin Zariya
Dan shekara saba'in da ake zargi da ake zargin dan bindiga ne a garin Zariya

Da yake bayyana hakan a sanarwar daya fitar a yau talata, kakakin rundunar ‘yan sandan jihar kaduna, mansur hassan, yace an kwato bindiga kirar ak-47 guda da wata karama kirar gida samfurin “pistol da harsashai 3.

Haka kuma, an kama wasu rikakkun masu garkuwa da mutane su 3 dake addabar al’ummar yankin arewa maso yammacin Najeriya.

A cewar kakakin rundunar ‘yan sandan, jami’an rundunar hadin gwiwa na shiyar Saminaka da mafarauta ne suka kama wadanda ake zargin da suka jima suna aiwatar da laifuffukan garkuwa da mutane da satar shanu da dama a karamar hukumar Lere ta jihar Kaduna.

Ya bayyana sunayen wadanda ake zargin da Isah Bappa Rabo daga kauyen Maibindiga da Ja’afaru Sale da Umar Musa dukkaninsu daga kauyen Durumi na karamar hukumar Leren jihar Kaduna.

A cewar kakakin ‘yan sandan, wadanda ake zargin sun amsa laifin zama cikin gungun masu garkuwa da mutane a karamar hukumar Lere kuma sun amsa laifin satar shanu, da suke sayar wa wani mai suna, Idris Abubakar, wanda shima an kamashi, sa’annan an kwato wasu shaidu da suka hada da bindiga kirar gida da adda da kuma wayoyin hannu guda uku.

Dandalin Mu Tattauna

XS
SM
MD
LG