Jami’an ‘yan sandan shiyar Tudun Wadan Zariya ne suka kama wanda ake zargin, mai suna Hussaini a unguwar Tudun Jukun sakamakon samun sahihan bayanan sirri game da take-takensa.
Al’amarin daya afku da misalin karfe 9 da rabi na safiya ya hada da wata tanka da ake zargin tana dauke ne da iskar gas wacce ta latse wata karamar mota tare da tarwatsewa a yayin da take kokarin shiga shatale-tale.
Ko da yake har yanzu babu cikakken bayanai kan harin, sai dai hukumomin sojin sun tabbatar da hakan a wata sanarwa da suka fitar a ranar Talata.
Shugaban kungiyar kwadago ta TUC Festus Usifo ne ya tabbatar da hakan a yau Talata a Abuja bayan wata ganawar hadin gwiwa na majalisar kolin manyan kungiyoyin kwadagon Najeriya 2.
Rahotanni daga kauyen farin Doki dake yankin Erana a karamar hukumar Shiroro na jihar Neja na nuna cewa, wani makeken rami da masu hakar zinari ke tona wa ya rufta da mutane akalla 50.
A babban birnin Abuja ma'aikatu, da bankuna, da ma sauran sassa da su ka shafi gwamnati sun kasance a rufe.
Duk da shigowar da Majalisar Tarayya tayi cikin zance a kurarren lokaci domin kaucewa shiga yajin aikin da aka ayyana a Juma’ar data gabata, tattaunawar ta cije, abinda ya kai ga fara yajin aikin.
Edun wanda ya kasance babban bako a shirin siyasar tashar talabijin ta Channels mai taken "Politics Today" a turance yace, tattaunawa akan batun mafi karancin albashi abune mai mahimmancin gaske karkashin tsarin dimokradiya.
A ranar Litinin din nan ne gamayyar kungiyoyin kwadagon Najeriya na NLC da TUC ke aukawa ckin wani gagarumin yajin aiki.
Shugaban Kungiyar Kwadago ta TUC, Festus Isifo ne ya ayyana shiga yajin aikin a yayin wani taron manema labarai daya gudanar tare da shugabannin kungiyar kwadago ta NLC a Abuja a yau Juma'a.
Sanarwar mai dauke da sa hannun shugaban kamfanin na riko, Victor Ojelabi, ta gargadi kwastomominsa da kodai su biya kudin wutar da suka sha ko kuma ya yanke musu ita.
Domin Kari
No media source currently available