Da irin kaso dake zuwa daga asusun tarayya, babu karamar hukumar da zata iya biyan naira dubu 62 a matsayin mafi karancin albashin da gwamnatin tarayya ta gabatar ballantana naira dubu 250 da hadaddiyar kungiyar kwadago ke bukata.
A yayin da damuna ta sauka kuma manoma sun fara ayukkan noma wasu wurare, gwamnatoci da kungiyoyin bayar da tallafi na kara tanke damara, wajen magance barkewar tashin hankali tsakanin manoma da makiyaya a Najeriya
Jami’an tsaro ne suka hallaka rikakken dan bindigar, wanda keda matukar hatsari tsakanin shugabanin ‘yan ta’addar arewacin Najeriya a shekarun baya-bayan nan, tare da wasu mutane 35.
Ya bayyana hakan ne a jiya Laraba yayin liyafar murnar cikar dimokradyiyar Najeriya shekaru 25 ba tare da tsaiko ba, a Abuja.
Babbar kotun tarayya dake Kano ta ce ta gamsu da hujjojin ta masu kara suka gabatar, saboda haka tana da hurumin sauraron shari'ar takaddamar sarautar Kano.
Hakan ya biyo bayan wa’adin sa’o’i 48 da gwamnatin jihar Kano ta ba ‘yan kasuwa da su fice daga kasuwar.
Tsohon mataimakin shugaban kasa Atiku Abubakar, kuma dan takarar shugaban kasa a jam’iyyar adawa ta PDP a zaben 2023 ya bayyana alhininsa a shafinsa na Twitter wanda aka sani da (X).
Lamarin ya faru ne a yayin wani artabu tsakanin sojoji da ‘yan bindiga.
Tinubu ya bayyana hakan ne a ranar Laraba a jawabinsa na ranar Dimokradiyya a yau Laraba 12 ga watan Yunin 2024 wanda tsohon shugaban kasa Muhammadu Buhari ya sauya zuwa duk ranar 12 ga watan Yunin shekara-shekara sabanin ranar 29 ga watan Mayun da aka saba a baya.
Gwamnan jihar Kaduna, Uba Sani ya bayar da umarnin a saki fursunoni 110 daga gidan gyaran hali da ke jihar, a zaman wani bangare na bikin ranar dimokradiyya na bana da kuma murnar cika shekara guda a kan karagar mulki.
Mai ba shugaban kasa shawara na musamman kan harkokin yada labarai Ajuri Ngelale ne ya sanar da hakan a wata sanarwa da ya fitar ranar Talata.
Domin Kari
No media source currently available