Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Kotu Ta Dage Shari'ar Cubana Game Da Zargin Wulakanta Naira


Cubana
Cubana

Babbar kotun tarayya da ke zamanta a Legas ta dage sauraron karar dan kasuwar nan mai suna, Pascal Okechukwu, wanda aka fi sani da “Cubana Chief Priest” har zuwa 25 ga watan Yuni domin ci gaba da sauraron shari’ar bisa zargin wulakanta Naira.

A ranar Laraba ne dai kotun ta dage zaman duk da cewar wanda ake tuhuma ba ya nan a kotun amma ya rubuta wasikar neman a dage sauraron karar.

A cikin wasikar da lauyoyin sa suka rubuta a madadin Cubana, sun tunatar da kotun cewa a zaman da ya gabata, bangarorin masu kara da karewa sun amince da a sasanta a wajen kotu.

Lauyoyi
Lauyoyi

Sun kuma sanar da kotun cewa tattaunawar ta yi tasiri kuma bangarorin za su kammala tattaunawa nan ba da dadewa ba.

Ba tare da wani korafi daga masu gabatar da kara ba, kotun ta dage zaman har zuwa ranar 25 ga watan Yuni domin samun rahoton sasantawar.

A ranar 17 ga watan Afrilu ne Hukumar Yaki da yi wa Tattalin Arzikin Kasa Ta’annati (EFCC) ta gurfanar da Okechukwu a gaban kuliya bisa zarge-zargen aikata laifuka uku da ake zarginsa da yin like da kudi da kuma wulakanta takardan Naira a wani taron jama’a da aka gudanar a otel din Eko da ke jihar Legas.

Hedkwatar Hukumar EFCC Da Ke Abuja
Hedkwatar Hukumar EFCC Da Ke Abuja

Ya ki amincewa da tuhumar da ake yi masa kuma aka bada belin sa akan kudi naira miliyan 10.

A tuhume-tuhumen, wanda ake karar, laifin ya ci karo da tanadin sashe na 21(1) na dokar babban bankin kasa na shekarar 2007.

Babban Lauyan Najeriya, Chikaosolu Ojukwu, ya shaida wa kotun cewa bangarorin na binciken yadda za a sasanta ba tare da kotu ba.

Mai shigar da kara na EFCC, Bilikisu Buhari, ta tabbatar da matakin kamar yadda lauyan wanda ake tuhuma ya bayyana, ya kuma shaida wa kotun cewa har yanzu hukumar na nazarin bukatar.

A watan Afrilu ne dai hukumar EFCC ta gurfanar da Idris Okuneye wanda aka fi sani da Bobrisky a gaban kuliya bisa irin wannan tuhuma da aka yanke masa na zaman gidan yari na watanni shida.

Wulakanta takardun kudin naira ko da kuwa ta yaya ne babban laifi ne.

Dokar Babban Bankin Najeriya 2007, ta hana liki, takawa, yin zane a kai, saidawa da ma lalata takardun kudi.

Dandalin Mu Tattauna

XS
SM
MD
LG