Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Hadakar Kungiyoyin Kwadago Sun Dakatar Da Yajin Aiki


NLC
NLC

Shugaban kungiyar kwadago ta TUC Festus Usifo ne ya tabbatar da hakan a yau Talata a Abuja bayan wata ganawar hadin gwiwa na majalisar kolin manyan kungiyoyin kwadagon Najeriya 2.

Hadakar kungiyoyin kwadagon Najeriya sun dakatar da yajin aiki na tsawon mako guda da suka tsunduma sakamakon gazawar kwamiti wajen samun matsaya akan batun mafi karancin albashi da karin kudin lantarki.

Shugaban kungiyar kwadago ta TUC Festus Usifo ne ya tabbatar da hakan a yau Talata a Abuja bayan wata ganawar hadin gwiwa na majalisar kolin manyan kungiyoyin kwadagon Najeriya 2.

Usifo ya shaidawa tashar talabijin ta Channels cewar, “ganawar hadin gwiwa ta majalisar kolin manyan kungiyoyin kwadagon najeriya na tuc da nlc ta amince ta jingine yajin aikin da mambobinta suka shiga tsawon mako guda ba tare da bata lokaci ba.”

Usifo ya kara da cewar, nan gaba kadan za’a fitar da sanarwar bayan taro.

Duk da shigowar da Majalisar Tarayya tayi cikin zance a kurarren lokaci domin kaucewa shiga yajin aikin da aka ayyana a Juma’ar data gabata, tattaunawar ta cije, abinda ya kai ga fara yajin aikin jiya Litinin.

Ma’aikata sun kauracewa wuraren aiki a fadin Najeriya sakamakon yajin aikin da kungiyar kwadago ta NLC da takwararta ta TUC suka tsunduma sakamakon karin kudin lantarki da kuma rashin cimma matsaya kan batun mafi karancin albashi.

Yajin aikin ya kassara harkokin kasuwanci da muhimman ayyuka a fadin Najeriya ciki harda makarantu da asibitoci da samarda wutar lantarki sakamakon biyayyar da ma’aikatan suka yi da umarnin kungiyoyin kwadagon nlc da tuc.

Tun daga jihar Rivers dake shiyar kudu masu kudanci zuwa Kaduna dake shiyar arewa maso yammacin Najeriya, ma’aikatan sun kassara harkokin tattalin arziki.

Al’amura sun tsaya cik a tashoshin jiragen saman Najeriya ciki harda na Abuja, Fatakwal, Kaduna da Legas.

Dandalin Mu Tattauna

XS
SM
MD
LG