Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Tinubu Ya Bai Wa Ministan Kudi Sa’o’i 48 Ya Gabatar Da Tsarin Biyan Albashi Mafi Karanci A Najeriya


Shugaban kasar Najeriya Bola Tinubu, Abuja
Shugaban kasar Najeriya Bola Tinubu, Abuja

Shugaban Najeriya Bola Tinubu ya umurci Ministan Kudi na kasar, Wale Edun, da ya gabatar da tsarin da gwamnati za ta bi na aiwatar da sabon adadin albashin ma’aikata mafi karanci.

WASHINGTON, D. C. - Ministan yada labarai na Najeriya, Mohammed Idris ne ya bayyana haka ranar Talata a Abuja bayan wakilan gwamnati masu tattauna batun sabon albashi sun gana da shugaban kasar.

Ministan yada labarai, Mohammed Idris (Hoto: Facebook/Ministry of Information)
Ministan yada labarai, Mohammed Idris (Hoto: Facebook/Ministry of Information)

“Shugaban kasa ya umurci Ministan Kudi da ya yi lissafi, ya gano yadda al’amarin zai kasance cikin kwana biyu, ta yadda za mu samu alkaluman da za mu sake tattaunawa da kungiyar kwadago”, acewar ministan.

Ministan ya kara da cewa “Shugaban kasa ya kuduri yin aiki da duk abin da kwamitin ya amince da shi. Ya kuma duba yadda zai kyautata walwalar ‘yan Najeriya.”

Idris ya kuma ce gwamnati ba ta adawa da karin albashi.

Tawagar gwamnatin tarayya ta hada da Ministan Yada Labaraim Idris, da Ministan Kudi, Edun, da Sakataren Gwamnatin Tarayya, George Akume da Ministan Kwadago Nkiruka Onyejeocha, da Ministan Kasafin Kudi da Tsare Tattalin Arziki, Atiku Bagudu da Shugaban Ma’aikatan Fadar Shugaban Kasa, Femi Gbajabiamila; da shugaban kamfanin NNPCL, Mele Kyari.

Mele Kyari
Mele Kyari

Tun da farko a ranar Talata, kungiyar kwadago ta dakatar da yajin aikin da ta ke yi a fadin kasar wanda ta fara da tsakar daren ranar Litinin bayan ta ki amincewa da tayin naira dubu sittin a matsayin albashi mafi karanci da gwamnati ta yi.

Dandalin Mu Tattauna

XS
SM
MD
LG