Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Sai Da Aka Kashe Na’urorin Daukan Hoto Kafin A Sace Daliban Kogi – Gwamna Ododo


Gwamna jihar Kogi Usman Ododo (Facebook/Usman Ododo)
Gwamna jihar Kogi Usman Ododo (Facebook/Usman Ododo)

Ododo ya bayyana hakan ne yayin da ya kai ziyarar ganewa idonsa jami’ar ta Confluence University a ranar Asabar.

Rahotanni daga jihar Kogin Najeriya na cewa an kashe duka na’urorin daukan hoto a jami’ar kimiyya da fasaha ta Confluence University da ke jihar kafin a sace wasu daliban makarantar a cewar Gwamna Usman Ododo.

A ranar Alhamis wasu ‘yan bindiga suka kutsa jami’ar wacce ke Osara suki sace dalibai tara cikin dare.

Ya zuwa lokacin hada wannan rahoto ba a ji duriyar daliban ko wadanda suka sace su ba.

Ododo ya bayyana hakan ne yayin da ya kai ziyarar ganewa idonsa jami’ar a ranar Asabar.

“Binciken da muka gudanar ya zuwa yanzu, ya nunacewa, duka na’urorin da muka saka an kashe su, kuma wannan ba wani abu ba ne illa zagon kasa daga mutanen cikin gida.” Ododo ya ce.

Gwamna Ododo ya yi kira ga iyayen daliban da su kwantar da hankulansu saboda jami’an tsaro suna bin diddigin al’amarin yana mai cewa bukatar gwamnati a yanzu shi ne a ceto daliban.

Batun satar dalibai a makarantun firaimare da sakandare da ma jami’o’i a Najeriya ba bakon abu ba ne musamman a arewaci.

‘Yan bindiga kan sace dalibai da dama su kutsa da su cikin daji har sai an biya kudin fansa kafin a sako su.

Satar mutane domin neman kudin fansa, babbar matsala ce a mafi aksarin jihohin arewa maso yammacin Najeriya.

Hukumomin kasar sun ce suna iya bakin kokarinsu wajen ganin sun shawo kan karshen wannan al’amari.

Dandalin Mu Tattauna

XS
SM
MD
LG