Cikin wata sanarwa da aka fitar a ranar Juma’a, wadda sakataren gwamnatin jihar Jigawa Alhaji Bala Ibrahim ya sanyawa hannu, gwamman jihar Umar Namadi, ya bada umarnin dakatar da kwamishinan ciniki da masana’antu Alhaji Aminu Kanta, bisa zargin sa da hannu a almundahana.
Yayin da al’umar musulmi ke daf da kammala ibadar Azumin Ramadana, aiwatar da shirin gwamnatoci na ciyar da mabukata a cikin wannan wata na cin karo da kalubalen zargin almundahana, inda ake tuhumar wasu daga cikin Jami’an gwamnati da hannu.
'Yan kungiyar Shi'a almajiran Sheikh Ibrahim Elzazzaky sun gudanar da zanga-zangar marawa Falasdinawa baya kan yakin Gaza a sassa daban-daban na arewacin Najeriya.
Karin kudin fito da Gwamnatin ta ce ta yi kan wutar lantarki ya jawo wani rudani wanda yasa Hukumar Kula da samar da Wutar Lantarki ta Najeriya wato NERC ta ci kamfanin rarraba wutar lantarki ta Abuja tarar Naira miliyan 200 saboda gazawa wajen bin ka'idojin da ta gindaya.
Wasu 'yan bindiga da ba'a san ko su wanene ba sun mamaye kauyen Agojeju odo dake Karamar Hukumar Omala ta jihar Kogi, inda suka hallaka mutane 19 tare da cinnawa gidaje da dama wuta.
Alkali Abimbola Awogboro na Babbar Kotun Tarayya dake Ikeja ya aika da Idris Olanrewaju da aka fi sani da Bobrisky zuwa gidan gyaran hali bayan daya amsa laifin wulakanta takardar kudi ta naira.
Al'ummomin dake zaune a garin Madaka ta jihar Nejan Nigeria inda 'yan bindiga suka hallaka kimanin mutane 60 a cikin makon Jiya sunce har ya zuwa wannan lokaci suna cikin yanayi na tashin hankali.
Mukarraban tsohon gwamnan jihar Kano, Abdullahi Umar Ganduje, sun mayar da martani ga yunkurin gwamnatin jihar mai ci, karkashin inuwar Jam’iyyar NNPP, na kafa kwamitocin bincike da kuma gurfanar da tsohon gwamnan a gaban babbar kotun jihar kan tuhumar badakalar wasu kudade.
Hukumar Da’ar Jami’an Gwamnati ta CCB ta dakatar da Shugaban Hukumar karbar korafe-korafe da yaki da cin hanci da rashawa ta jihar Kano, Muhuyi Magaji, daga ofishinsa biyo bayan tuhume-tuhume 10 na cin hanci da aka shigar hukumar a ranar 16 ga Nuwamban shekarar da ta gabata.
A yunkurinta na alkinta al'adu tare da dakile yaduwan laifuffuka, hukumar tace fina-finai ta Kano ta bada umarnin haramta tace fina-finai dake nunawa ko dabbaka dabi'un 'yan daudu ko harkar daba a fadin jihar.
Daruruwa kananan kungiyoyin manoma da masu sana’ar casar shinkafa da gyaran sauran kayayyakin noma a garuruwa da kayuka daban-daban na yankin arewacin Najeriya zasu ci gajiyar tsarin bada rancen kudi da babu ruwa na bankin duniya wadda aka kaddamar a jihar Jigawa.
Babban Sufeton 'Yan Sandan Najeriya, Kayode Egbetokun, ya sanarda kamen mutane 9 game da kisan jami'an 'yan sanda a yankin Ughelli na jihar Delta.
Domin Kari
No media source currently available
A jawabin da ya gabatar, shugaban kasar, Bola Tinubu ya ce gwamnatinsa na samun nasarar yaki da ta’addanci da kuma ‘yan fashin daji. Jawabin shugaban ya zo ne adaidai lokacin da matasa a wasu sassan Najeriya suka gudanar da zanga-zangar matsin rayuwa.
Mataimakan ‘yan takarar shugaban kasa, Tim Walz na jam’iyyar Democrat da kuma JD Vance na Republican sun fafata a muhawarar su ta farko wacce kuma ita ce kadai da za su yi kafin zaben shugaban kasa a watan Nuwamba. Ga fasaarar rahoton Tina Trinh daga New York.
A bana, sau biyu ana yin yunkurin halaka dan takarar shugaban kasa na jam’iyyar Republican Donal Trump. Muryar Amurka ta ji ta bakin wasu Amurka da suka mallaki bindiga wadanda suka ce yunkurin halaka Trump din bai sauya matsayarsu ba a game day dokokin mallakar bindiga a Amurka.