Wasu ‘yan bindiga sun kashe sarki mai daraja ta uku Abdulmutallib Nuhu a gidansa da ke wajen garin sansanin karamar hukumar Gasol ta jihar Taraba.
Sojojin Najeriya sun ceto wata mata da ‘yan Boko Haram suka yi garkuwa da ita shekaru goma da suka gabata a lokacin da take yarinya 'yar makaranta a kauyen Chibok, in ji rundunar a ranar Alhamis. An kuma ceto 'ya'yanta uku.
Al’ummar jihar Kogi a Najeriya da masana kundin tsarin mulkin kasar na ci gaba da yin tsokaci akan dambawar dake tsakanin tsohon Gwamnan jihar Alhaji Yahaya Bello da hukumar EFCC.
Jam’iyyar APC ta dauki matakin shari’a a kan mai shari’a Usman Na’abba na babbar kotun jihar Kano, inda suka mika koke ga majalisar shari’a ta kasa (NJC).
Yayin da cibiyar da ke yaki da yaduwar cututtuka ta Najeriya ke gudanar da bincike a kan wata cuta da ta bulla a Sakkwato, wadda ba a gane kanta ba, yanzu haka cutar na ci gaba da yaduwa .
Wani alkalin Najeriya zai yanke hukunci a wata mai zuwa kan ko ya kamata a dawo da belin jagoran 'yan awaren Nnamdi Kanu, a cewar Alkalin kotun ranar Laraba, bayan da a watan jiya kotun ta ki amincewa da sake shigar da kara tare da ba da umarnin fuskantar shari'a cikin gaggawa kan zargin ta'addanci.
Jami’an Hukumar Yaki da yi wa Tattalin Arzikin Kasa Ta’annati (EFCC) sun kai samame gidan tsohon Gwamnan jihar Kogi Yahaya Bello, da ke Wuse Zone 4 a Babban Birnin Tarayya Abuja.
Babbar kotun Kano karkashin jagorancin mai shari’a Usman Na’Abba ta bada odar dake tabbatar da dakatarwar da wasu shugabannin Jam’iyyar APC na mazabar Ganduje a karamar hukumar Dawakin Tofa su ka yi a shekaranjiya litinin.
Yau wata babbar kotun tarayyar Najeriya da ke zamanta a jihar Legas, ta bayar da belin wani dan kasuwa kuma mai ra’ayin jama’a, Pascal Okechukwu, wanda aka fi sani da Cubana Chief Priest, inda ta bukaci ya biya Naira miliyan 10, ya kuma gabatar da mutane biyu da za su tsaya masa.
A yayin da alkaluma suka yi nuni da cewa wasu kamfanonin jiragen saman waje sun shiga takun saka da kamfanin Airpeace, hukumar kula da kungiyoyin fararen hula ta Najeriya NCSCN da wasu masana tattalin arziki sun bukaci gwamnati ta tallafawa kamfanin na cikin gida.
Ofishin jakadancin Amurka a Najeriya ya shirya wani taro da nufin samar da daidaito tsakanin maza da mata, da kuma yadda za a karfafa mata. Ya kuma duba yadda ‘yan jarida ke ba da rahotannin abubuwan da suka shafi mata.
Kungiyar Kwadago ta kasa ta NLC tare da TUC ta ‘yan kasuwa, sun nemi gwamnati ta biya ₦615,000 ga ko wane ma’aikaci a matsayin mafi karancin albashi, sai dai wasu na ganin abu ne mai wuya idan an yi la'akari da zunzurutun bashin da ake bin Najeriya, wasu kuma suna ganin yaudara ce kawai.
Domin Kari
No media source currently available
A jawabin da ya gabatar, shugaban kasar, Bola Tinubu ya ce gwamnatinsa na samun nasarar yaki da ta’addanci da kuma ‘yan fashin daji. Jawabin shugaban ya zo ne adaidai lokacin da matasa a wasu sassan Najeriya suka gudanar da zanga-zangar matsin rayuwa.
Mataimakan ‘yan takarar shugaban kasa, Tim Walz na jam’iyyar Democrat da kuma JD Vance na Republican sun fafata a muhawarar su ta farko wacce kuma ita ce kadai da za su yi kafin zaben shugaban kasa a watan Nuwamba. Ga fasaarar rahoton Tina Trinh daga New York.
A bana, sau biyu ana yin yunkurin halaka dan takarar shugaban kasa na jam’iyyar Republican Donal Trump. Muryar Amurka ta ji ta bakin wasu Amurka da suka mallaki bindiga wadanda suka ce yunkurin halaka Trump din bai sauya matsayarsu ba a game day dokokin mallakar bindiga a Amurka.