An ce mai shari’a aneke yayi wani balaguron aiki, abinda ya sabbaba daga cigaba da sauraron shari’ar zuwa ranar 1 ga watan yuli mai zuwa.
Tsohon dan Majalisar da ke wakiltar mazabar Enugu ta Arewa kuma tsohon shugaban kwamitin yada labarai na Majalisar Dattawa, Sanata Ayogu Eze, ya rasu. Sanata Ayogu, ya rasu yana da shekaru 66 a duniya.
Wani mamakon ruwan saman da aka shatata da ya haddasa mummunar barna ga kurkukun mai matsakaicin tsaro dake garin Suleja na jihar Neja, abinda yayi matukar lalata gininsa.
Jami’an Amurka sun fara tantaunawa da shugabanin Majalissar CNSP mai mulkin Nijar da nufin tsara aiyukan ficewar dakarun Amurka 1,100 da ke girke a jihar Agadez yau shekaru sama da 10 a wani bangare na karfafa matakan yaki da ta’addanci a yankin Sahel.
Jami’an hukumar na farautar fursunonin da suka tsere kuma kawo yanzu sun samu nasarar cafke 10 daga cikinsu tare da taimakon wasu jami’an tsaro.
Hukumar yaki da cin hanci EFCC ta ce ta na sane da wani faifan bidiyo da a ka ga wani gwamna na watsa wa magoya bayansa kudi.
A cewar sanarwar da 'yan sandan yankin Bavaria suka fitar, gungun mai lakabin bakin gatari ko Black Axe" a turance nada hannu wajen aikata manyan laifuffuka a fadin duniya inda suka fi maida hankali a damfarar ta hanyar soyayya a kasar Jamus da halasta kudaden haram.
Peter Obi, wanda yayi hira da manema labarai a Abuja a yau Laraba, yace za’a iya cimma hakan ne ta hanyar magance matsalolin dake bangarorin ilimi da lafiya.
Harin na baya-bayan nan na zuwa ne kwanaki 5 bayan da ‘yan bindigar suka hallaka mutane 23 a anguwan danko ta yankin dogon dawa dake gabashin karamar hukumar Birnin Gwari.
Ma’aikatar, ta hannun Hukumar NCAA mai kula da sufurin jiragen sama a Najeriya, ta dakatar da ayyukan kamfanin jiragen saman, har sai an kammala cikakken bincike akansa.
Idan ba’a manta ba a ranar Laraba, 17 ga watan Afrilun da muke ciki ne, Onakoya ya fara kokarin kafa tarihin yin darar chess mafi tsawo inda ya shafe sa’o’i 60, al’amarin daya bashi damar rusa tarihin da wasu ‘yan kasar Norway 2 suka kafa a shekarar 2018.
Gwamnatin jihar Sakkwato da ke arewa maso yammacin Najeriya ta tube wasu sarakuna ciki har da 'yan majalisar sarkin Musulmi a kan dalilan da suka hada da rashin da'a da taimaka wa ayyukan ta'addanci.
Domin Kari
No media source currently available
A jawabin da ya gabatar, shugaban kasar, Bola Tinubu ya ce gwamnatinsa na samun nasarar yaki da ta’addanci da kuma ‘yan fashin daji. Jawabin shugaban ya zo ne adaidai lokacin da matasa a wasu sassan Najeriya suka gudanar da zanga-zangar matsin rayuwa.
Mataimakan ‘yan takarar shugaban kasa, Tim Walz na jam’iyyar Democrat da kuma JD Vance na Republican sun fafata a muhawarar su ta farko wacce kuma ita ce kadai da za su yi kafin zaben shugaban kasa a watan Nuwamba. Ga fasaarar rahoton Tina Trinh daga New York.
A bana, sau biyu ana yin yunkurin halaka dan takarar shugaban kasa na jam’iyyar Republican Donal Trump. Muryar Amurka ta ji ta bakin wasu Amurka da suka mallaki bindiga wadanda suka ce yunkurin halaka Trump din bai sauya matsayarsu ba a game day dokokin mallakar bindiga a Amurka.