WASHINGTON DC - Shugaban Hukumar, Abba El-Mustapha ne ya bayyana hakan a yayin wani taro tsakanin jami'an gudanarwar hukumar da masu ruwa da tsaki a masana'antar shirya fina-finan Hausa ta Kannywood.
A cewar kakakin hukumar tace fina-finan ta Kano, Abdullahi Suleiman, an yanke shawarar haramta tace irin wadannan fina-finai ne sakamakon karuwar damuwar al'umma game da mummunan tasirinsu akan matasa da gurbacewar al'adu.
Abba El-Mustapha ya jaddada mahimmancin kiyaye al'adu da dabi'u da tarrbiyar al'umma, inda yace: "lokaci yayi da zamu tace dukkanin fim din da zai gurbata mana al'adu, dabi'u da tarrbiya da sunan samun karin daukaka ko yawan masu kallo ko kuma neman kudi."
Matakin hukumar tace fina-finan ta Kano na zuwa ne a daidai lokacin da ake cigaba da mahawara a fadin Najeriya game da bukatar alkinta al'adu da bada damar fadin albarkacin baki da kuma kiyaye tarrbiyar al'umma.
A yayin da masu ruwa da tsaki a masana'antar shirya fina-finan Hausa ta Kannywood ka iya fuskantar kalubale wajen kiyaye wadannan sharuda, hukumar tace ba zata yi kasa a gwiwa ba wajen bunkasa kyawawan al'adun gargajiya.
Dandalin Mu Tattauna