KANO, NAJERIYA - Sai dai masana sunce matakin zai kawar da hankalin gwamnatin daga muhimman bukatun Jama’a.
A jiya ne gwamnan Kano Abba Kabir Yusuf ya kafa wasu kwamitoci guda biyu da aka dorawa nauyin bincikar yadda gwamnatin Abdullahi Umar Ganduje ta sarrafa kadarorin gwamnatin cikin shekaru 8 da suka shude, da kuma yadda aka samu tarzomar siyasa dama batan yara a wasu sassan jihar a lokacin gwamnatin ta Ganduje.
Kazalika, gwamna Abba Kabir Yusuf ya gurfanar da tsohon gwamna Abdullahi Umar Ganduje a gaban babbar kotun jihar bisa zargin rashawa da cin hanci na makudan miliyoyin naira da kudaden ketare na dala.
Barrister Haruna Isa Dederi shine kwamishinan shari’a kuma babban Atoni na jihar ta Kano ya yi karin bayani dangane da wannan mataki na gwamnati, “tun ranar da aka rantsar da mai girma gwamna, ya fada a gaban jama’a cewa, ya tarar da abubuwa marasa dadi wadanda suka shafi badakala da hakkokin jama’a, kuma zai bi sawu domin ya binciko abin dayake na al’uma ne, don haka ba bita da kulli ba ne batu ne daya shafi nauyi daya rataya a wuyan gwamnati.”
Sai dai a martaninsa ga wannan yunkuri, Dr Abdullahi Umar Ganduje tsohon gwamnan Kano kuma shugaban Jam’iyyar APC mai mulkin Najeriya ya bayyana matakin da cewa, gwamnan na Kano ne ke kokarin lullube gazawar sa a fagen shugabanci, domin kuwa duk da makudan biliyoyin Naira da gwamnatin tarayya karkashin jagorancin shugaba Bola Ahmed Tinubu ke turawa jihar Kano a kowane wata, har yanzu gwamnatin ta Abba Kabir Yusuf ba ta tabukawa Kanawa komai ba tsawon shekara guda da kama madafan iko.
A cikin wata sanarwa da sakataren labarun shugaban na APC Mr Edwin Olofu ya fitar, yace jahiltar tsarin doka da oda ta fuskar tafikar ayyukan gwamnati ne ya sanya Gwamna Abba Kabir Yusuf gurnafar da tsohon gwamna Ganduje a gaban kotu da irin wadannan tuhume-tuhume.
Shi-ma Dr Musa Iliyasu Kwankwaso, tsohon kwamishinan raya karkara a gwamnatin gwamna Ganduje yace, “wannan ba wani abu ne sabo ba a wurin ‘yan siyasa, ballantana azo ana cece-kuce. Mu abin daya dame mu a yanzu shine mutane suna cikin hali na yunwa, kamata yayi a fito a taimaki mutane, ba wannan labarin ake nema ba, kayayyaki da kudaden da gwamnatin tarayya ta Jam’iyyar APC ta turo Kano a taimaki al’uma shine abin daya damu mutanen Kano dana kasa baki daya.”
Sai dai masana harkokin siyasa da lamuran mulki sun fara fashin baki.
Dr Sa’idu Ahamd Dukawa Malami ne a jami’ar Bayero Kano na cewa, “komai dadewa, kamata idan mutum yayi laifi, ya girbi abin daya shuka, don haka a bincika laifukan da gwamnatin da ta wuce ta yi, a dauki mataki hukunci ba laifi ba ne, amma inda gizo yake saka shine idan za’a tuhumi gwamnatin data shude, sai anyi da ikilasi, ya zama gwamnatin da take tuhumar wadda ta gabace ta ba ta irin aikin ko laifin da take tuhuma an aikata a baya.”
Saurari cikakken rahoton Mahmud Ibrahim Kwari:
Dandalin Mu Tattauna