Ofishin jakadancin Amurka a Najeriya ya shirya wani taro da nufin samar da daidaito tsakanin maza da mata, da kuma yadda za a karfafa mata. Ya kuma duba yadda ‘yan jarida ke ba da rahotannin abubuwan da suka shafi mata.
Kungiyar Kwadago ta kasa ta NLC tare da TUC ta ‘yan kasuwa, sun nemi gwamnati ta biya ₦615,000 ga ko wane ma’aikaci a matsayin mafi karancin albashi, sai dai wasu na ganin abu ne mai wuya idan an yi la'akari da zunzurutun bashin da ake bin Najeriya, wasu kuma suna ganin yaudara ce kawai.
Kungiyar kare hakkin bil adama ta Amnesty International da sauran kungiyoyin kare hakkin bil adama a ranar Litinin sun yi kira ga gwamnatin Najeriya da ta dakatar da yarjejeniyar da kamfanin Shell ya yi na sayar da wasu kadarorinsa a matsayin wata hanya ta tabbatar da hakkokin al’ummar yankin.
Hukumar yaki da cin hanci da rashawa a Najeriya ta ce masu bincike a Najeriya sun kwato kusan dala miliyan 27 a wani binciken cin hanci da rashawa da ya shafi wata ministar gwamnati da aka dakatar da wasu jami'ai.
Mambobin jam’iyyar APC na mazabar Ganduje da ke karamar hukumar Dawakin Tofa a Jihar Kano sun dakatar da Shugaban Jam’iyyar APC na kasa Abdullahi Ganduje.
Iyayen 'yan matan Chibok sun bukaci a raba wasu daga cikin 'ya'yansu da a ka kubutar da tubabbun mazaje 'yan Boko Haram da ke zama da su a Borno karkashin kulawar gwamnati.
A ranar goma 14 ga watan Afirilun shekarar 2014 ne ‘yan ta’addan Boko Haram suka afka makarantar sakandaren gwamnati da ke garin Chibok a jihar Borno, su ka yi awon gaba da kimanin dalibai 276.
Rahotanni sun nuna cewa Mohammed Idris ya fadi kuma ya rasu jim kadan bayan kammala Sallar Idi a gidansa da ke Abuja ranar Laraba. Duk da kokarin farfado da shi, Allah ya yi masa rasuwa.
Tun a watan Janairu ne aka dakatar da Ministar Harkokin jinkai da yaki da fatara, Betta Edu, bisa zargin karkatar da kudaden jama’a da suka kai dalar Amurka 640,000 zuwa asusun banki na sirri.
Hukumomi sun ce tsakanin likitocin 15,000 zuwa 16,000 ne suka kaura a cikin shekaru biyar da suka gabata. Hakan ya bar kasar da ta fi fice a Afirka da likitoci 55,000 kacal ga al'umma miliyan 220.
Hukumar kula da lafiya ta Najeriya ta ce ta na janye wani rukunin ruwan maganin tarin yara na kamfanin Johnson & Johnson (JNJ.N), biyo bayan gano wani abu mai guba da ba a amince da shi ba, in ji ta ranar Laraba.
Gwamnatin jihar Katsina ta yi afuwan da sakin fursunoni 222 da ba za su iya biyan tarar da kotuna daban-daban ta yanke musu ba gabanin bikin Sallah.
Domin Kari
No media source currently available
A jawabin da ya gabatar, shugaban kasar, Bola Tinubu ya ce gwamnatinsa na samun nasarar yaki da ta’addanci da kuma ‘yan fashin daji. Jawabin shugaban ya zo ne adaidai lokacin da matasa a wasu sassan Najeriya suka gudanar da zanga-zangar matsin rayuwa.
Mataimakan ‘yan takarar shugaban kasa, Tim Walz na jam’iyyar Democrat da kuma JD Vance na Republican sun fafata a muhawarar su ta farko wacce kuma ita ce kadai da za su yi kafin zaben shugaban kasa a watan Nuwamba. Ga fasaarar rahoton Tina Trinh daga New York.
A bana, sau biyu ana yin yunkurin halaka dan takarar shugaban kasa na jam’iyyar Republican Donal Trump. Muryar Amurka ta ji ta bakin wasu Amurka da suka mallaki bindiga wadanda suka ce yunkurin halaka Trump din bai sauya matsayarsu ba a game day dokokin mallakar bindiga a Amurka.