WASHINGTON DC - Mutumin da ake zargi da zama dan koren ‘yan ta’adda, Tukur Mamu, wanda ke fuskantar tuhume-tuhumen ta’addanci a gaban kotu ya bukaci babbar kotun tarayya dake Abuja ta sauya wurin da ake tsare da shi daga hannun hukumar tsaro ta DSS.
Ya shigar da bukatar Mai Shari’a Inyang Ekwo ya sauya umarnin daya bayar na cigaba da tsare shi a hannun hukumar tsaro ta dss zuwa gidan yarin Kuje.
A cikin hujjar daya gabatarwa kotun ta hannun lauyansa abdul muhammad, Tukur Mamu yayi ikrarin cewar sau daya tak aka bari ya gana da likitansa wanda ya gabatarwa hukumar DSS bukatar gudanar da cikakkun gwaje-gwaje kiwon lafiya akansa.
Mamu yayi zargin cewar, tun bayar da aka gabatarwa hukumar DSS da rahoton likitan aka hana shi ganinsa kuma gashi yana bukatar ayi masa aikin tiyata a kowane irin asibiti a kasar nan.
Tukur Mamu ya cigaba da cewar yanayin lafiyarsa na kara tabarbarewa kuma zai iya rasa ransa kowane lokaci daga yanzu matukar ba’a dauke shi daga hannun hukumar tsaro ta DSS zuwa gidan yarin Kuje ba.
Ya kuma yi alkawarin cigaba da halartar zaman kotun game da tuhume-tuhumen da yake fuskanta akan ta’addanci inda yace saida rai zai iya halartar zaman kotun.
Daga bisani alkalin kotun ya tsaida ranar 20 ga watan Mayu mai kamawa domin zartar da hukunci akan bukatar Tukur Mamu.
Dandalin Mu Tattauna