WASHINGTON DC - Shugaban Najeriya Bola Tinubu ya jajantawa mutanen da ibtila’in fashewar iskar gas ya rutsa dasu a yankin Ita-Oshin na Karamar Hukumar Abeokuta ta arewa dake jihar Ogun.
Fashewar wacce ta samu asali daga wata tankar dakon gas ta fantsama zuwa sassan yankin, al’amarin daya sabbaba asarar rayuka da dukiya.
A sanarwar da hadiminsa akan harkokin yada labarai, Ajuri Ngelale, ya fitar, Shugaba Tinubu ya jajantawa gwamnati da al’ummar jihar Ogun game da afkuwar ibtila’in.
Ya kuma yabawa Gwamna Dapo Abiodun game da kokarinsa na shawo kan lamarin tare da dawo da kwanciyar hankula a yankin.
Shugaban kasar ya baiwa al’ummar jihar Ogun, musamman wadanda al’amarin ya shafa tabbacin samun agajinsa a wannan lokaci na alhin
Dandalin Mu Tattauna