ABUJA, NIGERIA - Cikin shekarun nan Sashen ya shahara wajen yada shirye-shirye da labaru masu ilimantarwa, fadakarwa harma da nishadantarwa, daga siyasa, lafiya, ilimi, shari’a, tattalin arziki da sauran su.
‘Yan siyasa da jami’an gwamnati dama kungiyoyi suna ta fadan ra’ayinsu.
Sanata Adamu Aliero ya ce VOA Hausa ta yi fice wajen wayar da kan jama'a kan sanin 'yancin su.
Shima Shugaban kungiyar muryar talaka Zaidu Bala Kofa Sabuwa ya ce ya shafe fiye da shekaru 20 ya na hulda da Sashen da ya zama masa tamkar makaranta; ya na mai addu’ar rahama ga wadanda suka rasu.
A na ta sharhin Zainab Muhammad Bununu ta ce Sashen ya taka rawar gani wajen wayar da kan mata musamman a bangaren siyasa.
Mai sauraron Muryar Amurka a yankin karkara Sulaiman Magama Gumau ya ce tashar ce ke kan gaba wajen wayar da al'ummar arewacin Najeriya.
A Najeriya da sanyin safiya za ka ga masu sauraro da ke shirin fita ayyukan yau da kullum su na sauraron shirin farko na kafar labarun ta duniya da karfe 6.00 don sanin halin da duniyar ke ciki.
Saurari cikakken rahotonr:
Dandalin Mu Tattauna