Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Mataimakin Shugaban Kasar Najeriya Ya Tafi Taron Tattalin Arziki Na Duniya


Mataimakin Shugaban Kasar Najeriya, Kashim Shettima (Facebook/Kashim Shettima)
Mataimakin Shugaban Kasar Najeriya, Kashim Shettima (Facebook/Kashim Shettima)

A ranar Lahadi ne mataimakin shugaban kasar Najeriya Kashim Shettima ya bar Abuja domin halartar taron shekara-shekara na dandalin tattalin arzikin duniya a Davos na kasar Switzerland da za a gudanar daga ranar 15 zuwa 19 ga watan Janairu, 2024.

WASHINGTON, D. C. - Shettima zai bi sahun sauran Shugabannin siyasa da na kasuwanci daga sassan duniya don halartar taron na tsawon mako guda.

Taron zai hada manya daga fannin siyasa, kasuwanci, al'adu da sauran shugabanni don tsara manufofin duniya, yanki da masana'antu

A cewar mai taimaka masa kan harkokin yada labarai, Stanley Nkwocha, a wata sanarwa da ya fitar a Abuja, mataimakin shugaban kasar zai kuma jagoranci kaddamar da wani shiri kamfanoni masu zaman kansu da ya shafi shirin cinikayya ba tare da shinge ba a nahiyar Afrika.

Ana kuma sa ran zai yi wata babbar tattaunawa da Manajin Darakta na Kamfanin Kudi na Duniya (IFC), Makhtar Diop da Firai Ministan Vietnam, Pham Minh Chinh, da dai sauransu.

Dandalin Mu Tattauna

XS
SM
MD
LG