Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Zaben Kano: Kotun Koli Za Ta Sanar Da Ranar Yanke Hukunci


Nasiru Yusuf Gawuna da Abba Kabir Yusuf
Nasiru Yusuf Gawuna da Abba Kabir Yusuf

Duk hukuncin da kotun ta yanke zai zama shi ne karshe kan wannan takaddama.

Kotun Koli da ke Abuja a Najeriya za ta sanar da ranar da za ta yanke hukuncin karshe a karar da Gwamnan Kano Abba Kabir Yusuf ya daukaka kan zaben gwamnan jihar.

Gwamna Yusuf na jam’iyyar NNPP, na kalubalantar hukuncin da kotun daukaka kara da kotun sauraren kararrakin zabe suka yanke wadanda suka ayyana Nasiru Gawuna na jam’iyyar APC a matsayin wanda ya lashe zaben jihar.

A ranar Alhamis kotun mai alkalai biyar karkashin jagorancin Alkali Joh Okoro, ta ce za ta sanar da ranar yanke hukuncin bayan kammala sauraren bangarorin biyu.

Duk hukuncin da kotun ta yanke zai zama shi ne karshe kan wannan takaddama.

A ranar 13 ga watan Nuwamba kotun daukaka kara ta amince da hukuncin da kotun sauraren kararrakin zabe ta yanke inda ta ce tsayar da Gwamna Yusuf da NNPP ta yi a takarar zaben ya sabawa dokar zabe.

A watan Satumba, kotun sauraren kararrakin zaben ta soke nasarar Yusuf a zaben da aka yi a ranar 18 ga watan Maris bayan da ta soke wasu kuri’un da ya samu.

Kotun ta soke kuri’a 165, 663 daga 1,019, 602 saboda babu hatimi a jikinsu, sannan ba a rattaba hannun akansu ba.

Hakan ya sa Yusuf ya garzaya kotun daukaka kara ya kuma dangana da kotun koli bayan da ya gaza samun biyan bukata.

Dandalin Mu Tattauna

XS
SM
MD
LG