Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Shugaban Gwamnatin Mulkin Sojan Nijar Ya Tsige Shugaban Hukumar Yaki Da Cin Hanci


Shugaban mulkin sojan Nijar Janar Abdourahamane Tiani
Shugaban mulkin sojan Nijar Janar Abdourahamane Tiani

Koda yake ba a bayyana dalilan yin haka a hukunce ba kwararru a harkar yaki da cin hanci na alakanta matakin da rashin gamsuwa da ayyukan hukumar, kuma a cewarsu har yanzu da sauran gyara muddin da gaske ake yakin.

A watan Satumban 2023 ne aka kafa hukumar yaki da cin hancin COLDEFF don maye gurbin hukumar HALCIA wacce ta gudanar da ayyuka na tsawon shekaru 12 da rabi na mulkin jam’iyar PNDS Tarayya da kawayenta.

A wannan lokacin Janar Tiani ya nada hafsan rundunar tsaro ta Jandarma Kanal Abdoulawahid Djibo a matsayin shugaban hukumar da ta kunshi wakilan alkalai lauyoyi da ‘yan farar hula wadanda kafin su kama aiki suka yi rantsuwa da Alkur’ani a bisa sharadin za su yi aiki da gaskiya, tare da rike sirrin aikinsu na farautar mahandama dukiyar kasa.

Sai dai kwatsam shugaban gwamnatin mulkin sojan ta Nijar ya tsige shgaban hukumar da mataimakansa, lamarin da kwararru a yaki da cin hanci suka ce da ma sun san za a rina.

Daga yanzu Hafsan tsaro na gandun daji Kanal Zennou Moussa Aghali ne zai jagoranci hukumar ta COLDEFF tare da nada wasu sabbin mataimaka.

Ba a dai bayyana dalilin wadanan sauye-sauye ba, to amma ‘yan fafutika na cewa matakin ba zai rasa nasaba da wasu matsalolin da ke tattare da ayyukan hukumar ba.

Masana sun yi gargadin cewa dole ne a dora hukumar ta COLDEFF kan turbar dokokin yaki da cin hanci na zahiri muddin ana son a cimma burin da ake hange.

A watan Janairun da ya gabata tsohon shugaban hukumar ta COLDEFF ya sanar cewa a tsawon watanni 12 hukumarsa ta samu billiyan 50 na cfa daga hannun mutanen da suka wawure dukiyar kasa.

Amma wasu ‘yan Nijar sun yi ta nuna rashin gamsuwa a bisa la’akari da makuddan kudaden da ake zargin an handame a zamanin gwamnatin farar hula wato daga 2011 zuwa lokacin da soja suka yi juyin mulki.

Saurari cikakken rahoto daga Souley Moumouni Barma:

Shugaban Gwamnatin Mulkin Sojan Nijar Ya Tsige Shugaban Hukumar Yaki Da Cin Hanci da Mukarrabansa
please wait

No media source currently available

0:00 0:03:29 0:00

Dandalin Mu Tattauna

XS
SM
MD
LG