Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Ana Ta Cece Kuce Kan Wasikun Kasashen AES Na Neman Tattaunawa Da ECOWAS.


FILE PHOTO: Mali junta calls for demonstrations to support decision to leave ECOWAS regional bloc
FILE PHOTO: Mali junta calls for demonstrations to support decision to leave ECOWAS regional bloc

Shugaban hukumar Kungiyar Kasashen Yammacin Afirka Dr Omar Alieu Touray, ya sanar cewa ya sami wasikun bukatar tattaunawa daga kasashe 2 cikin  mambobin kungiyar AES 3, duk da cewa tuni al’umomi da hukumomin kasashen suka yi bukin tabbatar da ficewarsu a hukumance.

Ana ci gaba da tafka mahawwara tsakanin masu goyon bayan ficewar Mali da Nijer da Burkina Faso daga CEDEAO da wadanda ke kushe matakin a jamhuriyar Nijer, bayan da shugaban hukumar gudanarwar kungiyar mai hedkwata a Abuja ya bayyana cewa kasashe 2 daga cikin kasashen AES 3 sun aike masa wasikar neman tantaunawa, koda yake bai fayyace sunayensu ba.

A wani taron manema labaran da ya Kira ta manhajar Zoom, washe garin cikar wa'adin ficewar wadanan kasashe 3 daga ECOWAS ko CEDEAO, shugaban hukumar kungiyar ta kasashen yammacin Afirka Dr Omar Alieu Touray, ya sanar cewa ya sami wasikun bukatar tattaunawa daga Kasashe 2 cikin mambobin kungiyar AES 3, duk da cewa tuni al’umomi da hukumomin kasashen suka yi bukin tabbatar da ficewarsu a hukumance.

Wani makusancin hambararriyar gwamnatin Nijar, Sahanine Mahamadou ya ce yanke alaka da ECOWAS abu ne mai kamar da wuya ga kasashen 3.

To sai dai, wakilin Sashen Hausa ya ce kakakin gamayyar Kungiyoyin FP masu goyon bayan gwamnatin CNSP Bana Ibrahim yana da shakku a game da ainahin abubuwan da wasikun kasashen na AES ke nufi, la’akari da shawarwarin da taron ministocin harkokin wajen kasashen 3 ya tsayar a Ouagadougou a jajibirin cikar wa’adin ficewar su daga ECOWAS na ranar 28 ga watan Janairun 2025, saboda haka magana ce ta tafiya kafada da kafada inji shi.

Wannan ba shine karon farko da wata kasa ta fice daga sahun kasashen ECOWAS ba, domin a shekarar 2000 kasar Mauritania ta fice daga kungiyar salum alum don shigar ta kungiyar Kasashen Larabawan yankin Maghreb kafin a 2017 ta shigar da bukatar neman amincewa ta sake komawa ECOWAS din, sai dai kawo yanzu ba ta sami amsa ba kamar yadda kasar Morocco da ta sami haye kujerar ‘yar kallo a shekarar 2005 ke jiran amsa a yanzu haka don samun izinin zama memba ta dindindin a kungiyar ta raya tattalin arzikin kasashen yammacin Afirka.

Domin a saurari rahoton Souley Moumouni Barma, a latsa nan:

CECE KUCE KAN BATUN WASIKUN KASASHEN AES.MP3
please wait

No media source currently available

0:00 0:03:04 0:00

Dandalin Mu Tattauna

XS
SM
MD
LG