Sabon fadan ya barke ne a makon daya gabata a jihohin Kordofan ta Kudu da Blue Nile tsakanin dakarun sojin kasar da wani tsagi na kungiyar SPLM-N, mai fafutukar neman ‘yancin al’ummar Sudan karkashin jagorancin Abdel Aziz Al-Hilu.
Jami’in Majalisar Dinkin Duniya mai kula da ayyukan jin kai a Sudan Clementine Nkweta-Salami yace an ba da rahotan cewa fada ya lakume akalla rayuka 60 a babban birnin jihar Kordofan ta Kudu Kadugli kadai.
Rundunar sojin Sudan da babbar abokiyar hamayyarta, RSF, sun jima suna gwabza yaki akan iko da kasar tun cikin watan Afrilun 2023, inda suka haddasa matsalar jin kai mai fadin gaske.
Dandalin Mu Tattauna